~ SHINE SHUGABAN 'YAN ADAM BAKI DAYA. ~SHINE MAI TUTAR YABO RANAR ALKIYAMA.
~ SHINE WANDA DUK ANNABAWA(AS) KE KASAN SHI(SAW).
~ SHINE FARKON MAI CETO.
~ SHINE ALLAH YAYI RANTSUWA DA RAYUWARSA(SAW).
~ SHINE WANDA DUTSE YAKE YI MASA SALLAMA.
~ SHINE WANDA KUTUTTURAN DABINO YAYI KUKA SABODA RABUWA DA SHI.
~ SHINE WANDA RUWA YA FITO TA TSAKANIN HANNUNSA(SAW).
~ SHINE WANDA AKA CIREWA WANI SAHABI IDO A WAJAN YAKI YA MAYAR MASA NAN TAKE KUMA YA WARKE NAN TAKE.
~ SHINE WANDA YAFI KOWA KYAWUN HALITTA.
~ SHINE WANDA YA FI KOWA KYAWUN HALI.
~ SHINE AKA AIKO GA DUK DUNIYA, AMMA
SAURAN ANNABAWA GA AL'UMMAR SU KAWAI.
~ SHINE WANDA KASA ZATA FARA TSAGEWA YA FITO RANAR ALKIYAMA.
~ SHINE WANDA AKA BAWA WASEELA DA FADEELA.
~ SHINE MAI TAFKIN KAUSARA.
~ SHINE WANDA ZAI FARA SHIGA AL-JANNAH
DA AL'UMMAR SA.
~ SHINE WANDA MUTUM DUBU 70 ZASU SHIGA ALJ-ANNAH BABU HISABI DAGA AL-UMMAR SA.
~ SHINE LITTAFIN SA YAFI DUKKAN LITTAFIN
DA AKA SAUKAR.
~ SHINE WANDA AKA HALASTAWA AL-UMMARSA GANIMA BAYAN TA HARAMTA GA WADANDA SUKA GABATA.
~ SHINE WANDA AKA HALASTAWA AL-UMMARSA SUYI TAIMAMA DA KASA.
~ SHINE WANDA AKA SANYAWA AL-UMMARSA KO'INA YA ZAMA MASALLACI.
~ SHINE WANDA AL-UMMARSA TAZO A KARSHE, AMMA TAFI WADANDA SUKA GABATA DARAJA.
~ SHINE WANDA YAYI ISRA'I DA MI'IRAJI HAR SUKA YI MAGANA DA ALLAH (T).
~ SHINE WANDA YAFI ANNABAWA YAWAN MABIYA DA YAWAN LADA.
~ SHINE WANDA AKA NINKAWA AL-UMMARSA AIKIN LADA.
~ SHINE MU'UJIZAR SA BATA YANKEWA.
~ SHINE WANDA DUK YA BISHI ZAI SHIGA AL-JANNAH; WANDA YA SABA MASA BAYA SO.
~ SHINE WANDA IDAN KAYI MASA SALATI
DAYA, ALLAH ZAIYI MAKA GOMA.
~ SHINE WANDA ALLAH YA SANYA MAKULLAN TASKOKIN KASA A HANNUNSA.
~ SHINE WANDA YAFI KOWA SON ALLAH KUMA ALLAH YAFI SONSA.
~ SHINE WANDA SAI KAFI SONSA, FIYE DA
IYAYANKA, DA YA'YANKA, DA KANKA, DA DUK
DUNIYA BAKI DAYA.
~ SHINE WANDA IDAN KAYI MASA SALLAMA,
ALLAH YAKE DAWO MASA DA RANSA YA AMSA MAKA SALLAMAR KA.
~ SHINE WANDA AKA SIFFANTA AL'UMMARSA DA ADALCI DA SHEDAR DA ZASU YIWA
ANNABAWA, AKAN SUN ISAR DA SAKO.
~ SHINE SAHIBUL MAKAMIL MAHMUD(SAW).
ALLAH YA KARA MANA SON ANNABI DA BIYAYYA A GARESHI.
ALLAH TSINEWA MASU TABA DARAJAR ANNABI(SAW)!!!
Sani Muh'd Sani Muh'd
Baban humaid Mnnu//Ng0027