HIZBULLAH TACE ZA TA RUBANYA KAI HARE-HAREN TA KAN ƘASAR TATSUNIYA




Shugaban Majalisar Zartarwar Hizbullah ya yi wa Ƙasar Tatsuniya kashedin cewa, ta kwana sanin cewa ayyukan da kungiyar ke kaddamarwa na soji za su karu ta hanyoyi da yawa.


Dubban jama’a ne suka hallara a yankin kudancin birnin Beirut a yau  Laraba domin janazar wani babban kusa na kungiyar Hizbullah Taleb Sami Abdallah (Abu Taleb), wanda ya yi shahada a wani harin da Ƙasar Tatsuniya ta kai ta sama a yammacin jiya Talata a Jwaya. kudancin Lebanon.


A jawabin da ya gabatar a wurin taron, shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sayyed Hashem Safieddine ya jaddada cewa yahudawan sahyuniya ba su koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya ba na yakin da suka yi da Hizbullah.


Ƙasar Tatsuniya ta dage da wautar ta… tana ganin cewa kashe shugabannin gwagwarmaya  zai raunana su ” in ji shi, yana mai nuni da cewa kwarewa ta nuna cewa Hizbullah tana kara karfi ne kawai kuma tana kara tsayin daka bayan shahadar shugabanninta.


Sayyed Safieddine ya jaddada cewa “dole ne Ƙasar Tatsuniya ta fahimci” cewa matakin da Hezbollah za ta dauka shi ne kara kai hare-hare a zirin Gaza, “a iri da yawa.

@ma'sumah Nigerian News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post