Yau Lahadi 25 ga wata Zul-qa'adah mai albarka, Wato a irin wannan ranar ne Ranar Dahwul ardi, ma'ana ranar da Allah (Swt) ya shimfida Kasa ta zauna daram a doron ruwa.
Allah (Swt) yana fada a cikin Littafinsa mai tsarki cewa:
"وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَاهَا"
"Kuma, ƙasa a bayan haka Ya Shimfida ta". Suratun-Naazi'ati aya ta 30.
An samo daga Imamu Ali ar-Rida (As) ya ce: " Daren 25 ga Zul-qa'adah shine daren da aka haifi Annabi Ibrahim (As) a cikinsa, kuma a daren ne aka haifi annabi Isah (As), kuma cikin sa Allah ya shimfida Kasa daga Karkashin Ka'abah, duk wanda ya azumci ranar kamar ya azumci watanni Sittin ne". Wasa'ilus-Shi'a hadisi na 4499.
A wata ruwayar ma akwai cewa: "Kuma a cikin sa ne Qa'im (ATF) zai bayyana"
Ya zo a ruwaya cewa: "Farkon rahamar da ta fara sauka daga sama zuwa Kasa, a cikin Ashirin da biyar ne daga watan Zul-qa'adah, duk wanda ya azumci wannan ranar kuma ya tsayu a cikin daren (Ya raya daren), yana da ladar ibadar Shekaru dari, wadan da ya azumci wuninsu ya kuma raya Dararensu".
Wasa'ilus-Shi'a juzu'i na 10 Shafi na 451.
WASU DAGA CIKIN AYYUKAN RANAR 'DAHAWUL ARDI':
1. An so a yi wanka a ranar.
2. Ana so a azumci ranar. Ranar tana daga cikin raneku 4 na shekara da aka karfafi azumtar su.
3. Akwai Sallah Raka'a 2 da ake yi da hantsi, kowace Raka'a Fatiha da Was-Shamsi 5, bayan Sallama a ce: LA HAULA WA LA QUWWATA ILLAH ALIYUL AZIM.
4. An so a Ziyararci Imam Ali Ar-ridha (As), An ambata cewa ziyararsa a irin wannan ranar yana daga cikin Ayyukan mustahabi mafi girma.
Da Fatan Yan Uwa Ba Zamu Manta damu Cikin Addu’o’insu Masu Albarka Ba.
Daga Shafin Sheikh Ahmad Yashi