Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane 150 A Jihar Neja

 


Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani kauye a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, inda suka kashe mutane takwas tare da yin garkuwa da kusan mutane 150 a wani sabon harin a jihar.


Hukumomin karamar hukumar sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, wasu maharan kan babura sun kai farmaki kauyen Kuchi da ke jihar Neja a daren Juma'a, inda suka kashe mutane takwas tare da yin awon gaba da mutanen kauyuka kusan 150.Hukumomin sun ce "Sun zo ne a kan babura kusan 100 kowannensu dauke da mutane uku." Babu wani taimako da ya samu a tsawon sa'o'i uku da suka yi cikin kauyuka."


Kungiyoyin da suka boye a dazuzzukan jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja, sun yi kaurin suna wajen sace-sacen mutane, ciki har da dalibai da yawa a makarantu a shekarun baya-baya nan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post