@-MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce yadda al’ummar Iran suka fito dafifi wajen jana’izar marigayi shugaba Ibrahim Raeisi ya nuna irin karfin da Jamhuriyar Musulunci take da shi.
Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da ya kai ga iyalan marigayi shugaban kasar da ya rasa ransa tare da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian da wasu mukarabansa shida a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a lardin Azarbaijan da ke arewa maso yammacin kasar Iran a ranar Lahadi.
Jagoran ya ce irin yadda al’ummar Iran suka halarci tarukan jana’izar marigayi shugaban kasar sako ne ga duniya na goyon baya ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa, karfin Jamhuriyar Musulunci yana fitowa ne daga al’ummar Iran.
” ko yadda baki daga kasashen duniya daban daban suka halarci jana’izar, ya nuna farin jinin Jamhuriyar Musulunci da karfinta” inji shi.
Mummunan hatsarin jirgin saman na Helikwabta da ya faru ga shugaban kasar da mukarabansa ya jefa al’ummar Iran cikin dimuwa da bakin ciki.