RAHOTO NA BIYU DANGANE DA HATSARIN JIRGIN SAMAN DA YA KAI GA SHAH ADAR SUGABA RA,ISI

 


A rahoto na biyu wanda kwamitin da sojojin kasar Iran suka kafa don bincike da gano musabbabin faduwar jirgin shugaban kasa a ranar Lahadi 19 ga watan Mayu, ya nuna cewa hatsari ne jirgin yayi.


Kamfanin dillancin labarai Iran press na kasar Iran ya Gholam-Hussain Esma’ili shugaban ma’aikata a ofishin shugaban kasa yana fadar haka a Jiya Laraba. 


Ya kuma kara da cewa kwamitin ya fidda bayanai na asali wadanda suka shafi faduwar jirgin, kuma nan gaba za’a fidda cikekken bayanin kan hatsarin.


A ranar lahadi 19 ga watan Mayu ne jirage guda ukku, dayansu dauke da shugaban kasa, Ministan harkokin waje, wakilin Jagora a jihar Azarbajan ta gabsa, gwamnan Azarbaijan ta gabas, da nasu gadin shugaba kasa, matuka jirgi da masu khdima yayi  hatsari a kan hanyarsu ta dawowa Tabriz daga kasar Azarbaijan, inda aka kaddamar da wata madatsra ruwa.


Sanadiyyar wannan hatsarin dai shugaban kasa da dukkan wadanda suke tare da shi sun rasa rayukansu .


Rahoton ya kara da cewa a wannan rahoton na biyu sun yi bincike kan inda suka sami jikin jirgin babba da kuma inda suka sami sauran bangarensa da kuma mutanen da suke cikinsa na nuna cewa jirgin ya dake jikin dotse ne sannan ya fadi kasa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post