LADUBBAN YIN SHUKA DA DASHAN BISHIYA A BISA KOYARWAR AHLUL BAITI (AS)



Babu wani abu da Limaman shiriya (as) ba su koyar da al“umma ba,abunda ke tafe Hadisai  ne dangane da shuka da dasa Bishiya:-


1.Imam Sadiq (as)yana cewa:“A yayin da kake so ka yi shuka,ka debi damqi na iri  hannunka sannan ka kalli Gabas kace:”Afara“aitum ma tahrusun,a“antum tazra“unahu am nahnu zari“un“ sau uku za a fadi hakan“Sannan kace:“Allahumma ij“alhu Habban Mubarakhan warzuqna fihi salama“Sannan sai ka shuka abun shukar taka.


2.Daga Imam Sadiq (as) yana cewa:“A yayin da ka za ka yi shuka kace:“Ya Allah hakika na yi bizne iri,kai ne mai fitar da shi ka sanya shi ya zamanto qwaya mai rubanyuwa


3.Imam Sadiq (as) yana cewa:“A yayin da za  ka yi shuka kace:“Subhanal Ba“isul Waris“ idan ka yi haka ba zai ki fitowa ba insha Allahu.”


Ka da a manta sad da za fara aikin shukar,a karanta suratil Fatiha da yin salati.


Allah ya sanya albarka a daminar nan,ya tsare mu daga sharrinta.


Alhamis 30/5/2024

By Ustaz Sulaiman Bullet

@Ma'asumah Nigerian News Update



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post