Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya tabbatar da cewa: Marigayi shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya dauki nauyin siyasa kan harin mayar da martini na “Alkawarin Gaskiya” da Iran ta kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila.
Manjo Janar Hussaini Salami ya bayyana cewa: Babban taro wajen jana’izar shugaban shahidai Ibrahim Ra’isi ya dakile shirin makiya.
Manjo Janar Salami ya ce: Dole ne a fahimci cewa: Makiya sun gudanar da duk wani shiri na kai farmaki kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma sun yi amfani da matsin lamba daban-daban wajen yin hakan, sannan sun yi amfani da karfin soji da kafafen yada labarai wajen haifar da baraka a tsakanin al’ummar Iran da kuma raba wannan al’umma da tsarin juyin juya halin Musulunci, amma hakarsu bata cimma ruwa ba.
Sannan a yau ana ganin dukkanin al’ummar Iran sun halarci jana’izar wadannan shahidai da suka shugabance su, kuma hakan wani dalili ne na alfahari da daukakar kasar Iran.