KASAR YEMEN TA KAKKABO JIRGIN YAKIN SAMFURIN MQ-9 NA AMURKA A KARO NA 5,

 



Majiyar sojojin kasar Yemen ta bada sanarwan kakkabo jirgin yaki kuma na leken asiri samfurin MQ-9 wanda ake sarrafashi daga nesa mallakin kasar Amuraka a cikin lardin Ma’arin na kasar a jiya da yamma.


Kamfanin dillancin labaran Iran Press na kasar Iran ya nakalto CENTACOM cibiyar bada umurni na kasar Amurka na tabbatar da labarin faduwar jirgin a lardin Maarib mai tazarar kilomita 120 daga birnin San’aa babban birnin kasar.


Kamfanin dillancin labaran AP na kasar Faransa ya ce hotunan jirgin sun nuna shi kwace a kan cikinsa sannan bindinsa a rabid a jikin.


Sojojin Amurka da Burtania sun shiga yaki da kasar Yemen kai tsaye ne bayan fara yakin Tufanul Aksa a yankin Gaza na Falasdinu, kuma gwamnatin Amurka ta shiga yaki da Yemen ne don hanata cilla makamai kan jiragen ruwan daukar kaya wadanda suke wucewa da babul Mandam na kasar Yemen, suke kuma nufin HKI sai in har an dakatar da yaki a Gaza.


Wannan shi ne jirgin yaki Irinsa na 5 wadanda sojojin kasar Yemen suka kakkabo a sararin samaniyar kasar, ton lokacinda Amurka da kawayenta suka fara yakarta.


Kamfanin labaran tsaron sararinsamanbiya na kasar Amurka da farko ya tabbatar da faduwar jirgin amma ya kara da cewa mai yuwa sojojin Yemen sun kwace iko da jirgin sannan suka saukar da shi a inda ya fadi tare da amfani da tsarin GPS.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post