KADAN DAGA CIKIN ILLAR MINING




1. Dauke Hankalinmu game da Kisanmu da ake wadda Kuma kowa ya sani kashe² da ake a Nigeria kwangila ce daga Turawa. Wadda Kuma kullum karuwa yake ba raguwa ba.

2. Dauke Hankalinmu wajen Kulawa da Addini.( Karatun Qur'an Azkar, Nafila, sauraron Wa'azi).

3. Koyawa Mana lalaci da nufin Samun kudi ba tare da Shan wahala ba.

4. Halasta Mana kudi kowane iri ba tare da tantance Halak da Haram ba.

5. Daukaka Darajar Yahudawa a dalilin sun ba ka hanyar samun kudi cikin sauki.

6. Cusawa Yara  akidar amfani da waya wadda hakan kan Hana Yara yin karatu.

7. Koya Mana Raina Sana'o'i Musamman Kananan Sana'o'i.

8. Rashin Kulawa da Mazaje daga matar aure .

9. Rashin Bai wa Mata lokaci daga mazajensu. 

10. Rashin Kulawa da Kuma ba da muhimmanci ga Mai sana'a(a kasuwa ko shago).

11. Samun gazawa daga ma'aikatan gwamnati, sakamakon Mining.

12. Saka Buri a zuciya a kan abin da ba shi da tabbas Kuma ba naka ba.

 

Wannan kadan kenan daga ciki, na sani wani zai ce min dan kauye, ko Kuma ban waye ba, to wallahi sai dai a fada domin har a Raina ban yarda da wannan tsarin ba. Dalilina anan shi ne, ta Yaya wani zai ba ka kudi ba tare da wata manufa da yake son cimma Kansa a kanka ba??? 


Mutanen Nan YAHUDAWA a duk duniya ba su da MAKIYI Kamar Musulmai da Kuma Bakar Fata, to ta Yaya za su so ku amfana da arzikinsu haka kawai??? 


Sannan ku Kara tunani da kyau,

Misali Zan ba ka, yanzu a ce  ka mutu, sai Allah ya tambayeka a Ina ka samu wannan kudin, me za ka ce masa,??? Ko dai ba ka yadda da za a Yi maka wannan tambayar ba ne, a Ina ka samo?? Me ka Yi da su??? Ko dai mining din ya mantar da mu wannan??.


Dan Uwa/'yar uwa wallahi Kar mu ruda kanmu, mu Yi taka-tsantsan da wannan rayuwa, domin fa abin akwai ban Tsoro, yanzu daga jin NOTCOINS ta fashe duk mutane sun rude, kowa Kudi kawai, maza da Mata Yara da manya. 


Allah ya Fahimtar da mu bihaki Muhammad Ali wa,Ali Muhammad 

@Ma'sumah Nigerian News Update





Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post