Jagoran juyin juya halin musulunci Na Ƙasar Iran Imam Ayatullahi Sayyid aliyul Khaminae ya fadawa daliban jami’o’in Amurka wadanda suke goyon bayan al-ummar Falasdinu a yakin da gwamnatin kasarsu take da hannu dumudumu a cikinsa, kan cewa suna bisa bangaren da yake da gaskiya a tarihi.
Tashar talabijin ta Presstva a Tehran ta nakalto jagoran yana fadar haka a wata wakisa ta musamman da ya rubutawa daliban a yau Alhamis.
Wasikar taci cewa Gaba Da cewa, kuna cikin wadanda suke gwagwarmaya don taimakawa wadanda aka zalunta kuna kuma turjiya ga azzaluman shuwagabannin kasar Amurka wadanda suke bawa HKI duk tallafin da take bukata a yakin da take fafatawa a Gaza.
Daga karshen jagoran ya bayyana cewa yana tare da su a matsayin da suka dauka.
Tun cikin watan Afrilun da ya gabata ne dubban daliban jami’o’i a kasar Amurka da wasu kasashen yamma suka fara zaman dirshen a cikin harabobin jami’o’insu don tursasawa gwamnatocin kasashensu su dakatar da tallafin da take bawa HKI, sannan su kawo karshen yaki a gaza.