Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Barazanar nukiliyar yahudawan sahyoniya na iya canza koyarwar Iran kan batun nukiliya
Sakataren majalisar kula da harkokin kasashen waje ta Iran Abbas Arakchi ya bayyana cewa: Barazanar yin amfani da makamin nukiliyar da yahudawan sahayoniyya suke yi na iya sauya akidar Iran game da batun mallakar makamin nukiliya.
A cikin bayanin da ya gabatar a wajen zaman taron tattaunawa kan ire-iren ci gaba da aka samu a yankin Gabas ta Tsakiya bayan harin daukan fansa da Falasdinawa suka kaddamar kan haramtacciyar kasar Isra’ila na “Ambaliyar Al-Aqsa”, jami’in na kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana sanarwa da babbar murya cewa tana goyon bayan gwagwarmayar Falastinawa ta kowace fuska kuma ba ta jin kunyar bayyana hakan ko kadan.
Yana mai nuni da cewa: Barazanar yin amfani da makaman nukiliyar da yahudawan sahayoniyya suke yi, zai iya sauya matakan tsaro a yankin tare da tilastawa wasu sake yin nazari kan matsayinsu na baya game da makamashin nukiliyarsu na zaman lafiya.
@Ma'asumah Nigerian News Update