IRAN TA JADDADA ANIYAR TA Na TALLAFAWA KUNGIYOYIN FALASDINAWA,



Shugaban rikon kwarya a kasar Iran ya jaddada cewa: Tsarin Iran na tallafawa kungiyoyin gwagwarmaya ba zai canza ba


Shugaban rikon kwarya da ke tafiyar da harkokin shugabancin kasar Iran Muhammad Mokhber ya jaddada shirin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da goyon baya ga tsayin dakar al’ummar Falastinu da neman hakkokinsu wanda marigayi shugaban kasa Sayyid Ibrahim Ra’isi da ministan harkokin wajensa Hossein Amir Abdollahian suka tafi a kai, yana mai jaddada cewa: 


Tsare-tsaren Jamhuriyar Musulunci ta Iran na asali sun ginu ne kan tallafawa kungiyoyin gwagwarmaya musamman kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa kuma manufofi ne da ba zasu taba canzawa ba.


Mokhber ya jaddada hakan ne a zantawarsa da babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami Ziyad al-Nakhalah ta hanyar wayar tarho, inda Muhammad Mokhbir ya nuna jin dadinsa ga juyayi da alhinin Ziyad al-Nakhalah ya yi ga gwamnati da al’ummar Iran biyo bayan shahadar Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa.

@Ma'asumah Nigerian News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post