Da Ɗumi Ɗumi: Rundunar Sojan Iran Sun Fitar Da Rahoton Farko Kan Hatsarin Jirgin S. Ra'isi




Babban Hafsan Sojojin Iran ya fitar da rahoton farko kan wasu muhimman bangarori da kuma dalilan da suka haddasa hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu na baya-bayan nan da ya kai ga shahadar shugaba ƙasar Ebrahim Raeisi da tawagarsa. 


An fitar da rahoton ne a ranar jiya Alhamis da wanda ke yin karin haske kan lamarin da ya faru ranar Lahadin da ta gabata, inda Raeisi da tawagarsa da suka hada da ministan harkokin wajen ƙasar HosseinAmir-Abdollahian suka yi shahada bayan da jirgin da ke dauke da su ya yi hadari a arewa maso yammacin kasar Iran, ranar Lahadi.


Rahoton ya ce an aike da wata tawagar bincike domin duba wajan da  hatsarin ya afku a ranar Litinin. Tawagar, tace, ta yi nasarar tattara “wani bangare mai ban mamaki” na bayanan da take bukata don bincika abubuwan da ka iya haifar da lamarin. Rahoton ya ce jirgin mai saukar ungulu dauke da manyan mutanen ya yi hadari ne a lokacin da ya ke tafiya a kan hanyar da aka tsara shi, inda ya ce jirgin bai kauce hanya ba.


Rahoton ya ƙara da cewa shi jirgin mai saukar ungulu ya kama wuta ne bayan da ya fado wani yanki mai tsaunuka, ya kuma bayyana sun duba dukkan tarkacen jirgin ba su dauke da kowanne nau'in harsashi ko alamun tasirin makamancin haka, a cewar rahoton, wasu jiragen ɗaukan hoto marasa matuƙa na Iran ne suka gano wurin da hatsarin ya afku da misalin karfe 05:00 na safiyar ranar Litinin,


Kuma nan take jami'an bincike sun isa wurin ba da dadewa ba. Sadarwar da aka yi kafin abin da ya faru tsakanin jirgin da ma'aikatar kula da kasa ba ta ƙunshi wani abin "shakku" ba, ya ce, za a sanar da al'ummar ƙasar game da duk wani binciken da aka samu a kan lokaci.


Fassarar Rahoton Press TV


—Bilya Hamza Dass

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post