Sojojin HKI biyu ne suka halaka a lokacinda wani bafalasdine ya Burma cikinsu da motarsa, a wani wurin bincike a raewacin yankin yamma da kogin Jordan.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto wata kafar yada labarai ta yahudawan tana fadar haka a jiya Lraba. Ta kuma kara da cewa, rahoton ya ambaci wurin da abin ya faru da suna ‘wurin bincike na Awarta dake kusa da birnin Nablos.
Labarin ya nakalto shafin yanar gizo na labarai mai suna Walla na yahudawan na cewa, gwamnatin HKI ta tura sojojin sama da na kasa don gano wanda ya aikata hakan. Wannan harin yana zuwa ne a dai dai lokacinda sojojin HKI suke kara tsananta hare haren da suke kaiwa Falasdinawa a gaza musamman a garin Rafah na kudancin yankin.
Tun ranar 7 ga watan Octobvan day a gabra ne sojojin HKI suke kisan kiyashi ga al-ummar Falasdinu , wanda ya zuwa yanzu sun kashe mutane 36,170 ko kuma kimani mutum 40,000 idan an hada da wadanda suka bace. Mafi yawansu mata da yara. Banda haka wasun fiye dubu 80 sun ji rauni.