MAZA AKA SANI DA KISHI, MATA SAI DAI HASSADA !!!

 

      @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DALILIN DA YASA AKA BAWA MAZA DAMAR AUREN MATA HUDU YAYIN DA AKA HARAMTAWA MACE AUREN MAZA BIYU 

Da yawa za kaji mace na zaqewa akan mijinta da cewa tana yin kishinsa ne yasa ba ta son ganinsa da wata mace, hakan kuwa kan sa wasu mazan su dauki wannan yaudara.

Tabbas wannan magana da suke yi ba gaskiya bane, hassada suke yiwa 'yan'uwansu mata don kada su sami abokan zama kamar yadda su suka samu. Namiji ne wanda Allah ya sanya masa kishi amma ba ga mace ba kamar yadda za mu gani cikin wannan rubutu namu. 

DALILIN DA YASA ALLAH YA 'DORA KISHI KAN MAZA 

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

٣٧- عِدَّةٌ مِنْ أَصْحَابِنَا عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ خَالِدٍ عَنْ عُثْمَانَ بْنِ عِيسَى عَنْ بَعْضِ أَصْحَابِنَا عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ عَلَيْهِ السَّلَامُ قَالَ: لَيْسَ الْغَيْرَةُ إِلَّا لِلرِّجَالِ، فَأَمَّا النِّسَاءُ فَإِنَّمَا ذَلِكَ مِنْهُنَّ حَسَدٌ وَ الْغَيْرَةُ لِلرِّجَالِ وَ لِذَلِكَ حُرِّمَ عَلَى النِّسَاءِ إِلَّا زَوْجُهَا وَ أُحِلَّ لِلرِّجَالِ أَرْبَعاً، فَإِنَّ اللَّهَ أَكْرَمُ مِنْ أَنْ يَبْتَلِيَهُنَّ بِالْغَيْرَةِ وَ يُحِلَّ لِلرَّجُلِ مَعَهَا ثَلَاثاً.

Daga Iddatu daga Sahabbanmu daga Ahmad Bn Muhammad Bn Khalidi, daga Usmana Bn Isah, daga sashen Sahabbanmu daga Abu Abdullah (A. S) yace :

" BABU KISHI SAI GA MAZA, AMMA MATA HAKAN A GUNSU HASSADA CE. KISHI GA MAZA YAKE, SABODA AKA HARAMTAWA MATA (wani mutum) IN BA MIJINTA BA. AN HALATTAWA MAZA (auren mata) HUDU, DOMIN ALLAH YA KARRAMA DON YA JARRABE SU DA KISHI, KUMA YA HALATTA GA MUTUM UKU TARE DA ITA ."

Kunga anan tunda an haramtawa mace kasancewa da wani namiji in ba mijinta ba, to, dole idan namiji yaga matarsa tare da wani yayi kishin haka. Ita kuwa tunda ta san Allah ya hallatawa mijinta auren mata hudu, bai kamata ace taji wani abu in ta gan shi da wata ko yana shirin kawo wata ba. Saboda haka in har kaga tana tayar da qayar baya da nufin kishi qarya ne, ita dai kawai tana yiwa wancan matar hassada ce. 

A wata riwayar kuma tana cewa:

٤٠- فِي عُيُونِ الْأَخْبَارِ فِي بَابِ مَا كَتَبَ بِهِ الرِّضَا عَلَيْهِ السَّلَامُ إِلَى مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ فِي جَوَابِ مَسَائِلِهِ فِي الْعِلَلِ: وَ عِلَّةُ تَزْوِيجِ الرَّجُلِ أَرْبَعَ نِسْوَةٍ وَ تَحْرِيمِ أَنْ تَزَوَجَ الْمَرْأَةُ أَكْثَرَ مِنْ وَاحِدٍ، لِأَنَّ الرَّجُلَ إِذَا تَزَوَّجَ أَرْبَعَ نِسْوَةٍ كَانَ الْوَلَدُ مَنْسُوباً إِلَيْهِ، وَ الْمَرْأَةُ لَوْ كَانَ لَهَا زَوْجَانِ أَوْ أَكْثَرُ مِنْ ذَلِكَ لَمْ يُعْرَفِ الْوَلَدُ لِمَنْ هُوَ، إِذْ هُمْ مُشْتَرِكُونَ فِي نِكَاحِهَا وَ فِي ذَلِكَ فَسَادُ الْأَنْسَابِ وَ الْمَوَارِيثِ وَ الْمَعَارِفِ، وَ عِلَّةُ تَزْوِيجِ الْعَبْدِ اثْنَتَيْنِ لَا أَكْثَرَ مِنْهُ لِأَنَّهُ نِصْفُ رَجُلٍ حُرٍّ فِي الطَّلَاقِ وَ النِّكَاحِ لَا يَمْلِكُ لَهُ نَفْسُهُ وَ لَا لَهُ مَالٌ، إِنَّمَا يُنْفِقُ عَلَيْهِ مَوْلَاهُ وَ لِيَكُونَ ذَلِكَ فَرْقاً بَيْنَهُ وَ بَيْنَ الْحُرِّ، وَ لِيَكُونَ أَقَلَّ لِاشْتِغَالِهِ عَنْ خِدْمَةِ مَوَالِيهِ.

Ya zo cikin Uyunul-Akbaar cikin Babi wanda Imam Ridha (A. S) ya rubuta zuwa ga Muhammad Bn Sinaan cikin jawabi na mas'ala kan Illoli : Da illar namiji ya auri mata hudu (4) da haramcin mace ta auri fiye da daya (1) . (Yace :

" DOMIN SHI NAMIJI IDAN YA AURI MATA HUDU (4) (dukkan) 'DAN DA ZA A HAIFA ZA A JINGINA SHI NE ZUWA GA ZUWA GARE SHI. ITA KUWA MACE DA ZA ACE TANA DA MAZAJE BIYU (2) KO FIYE DA HAKA, TO, DA BA ZA ASAN 'DAN NA WAYE BA DAGA CIKINSU, DOMIN SUNYI TARAYYA WAJEN AURENTA. KUMA CIKIN HAKA ZA A SAMI LALACEWAR NASABA DA GADO DA SANI (asalin wannan abinda aka haifa). 

KUMA ILLAR BAWA YA AURI BIYU BA YA YIWUWA, DOMIN SHI (bawan) RABIN MUTUN 'YANTACCEN NE CIKIN SAKI (divorce) DA AURE. BAI MALLAKI KANSA BA KUMA BA SHI DA DUKIYA. ABIN SANI MAIGIDANSA NE KE CIYAR DASHI DOMIN HAKAN RABEWA NE TSAKANINSA DA TSAKANIN MAI 'YANCI. KUMA DOMIN YA KASANCE MAFI QARANCI WAJEN SHAGALTUWARSA DAGA YIWA UBAN GIDANSA HIDIMA. "

تفسير الصافي، ج١، ص: ٤٢٠

Cikin riwayar farko za muga an fada mana dalilin da yasa Namiji ne aka sanyawa kishi, domin babu wanda zai taba jin dadi ace wani na tarayya da abinda shi kadai ne ya kamata ace yana tarayya dashi. Saboda haka sai ya zama ita mace ba a sanya mata kishi ba saboda dama ita ba ayi ta don ta kasance tana zama ita daya (1) qarqashin namiji ba . Saboda haka duk abinda kaga tana yi kan mijinta don ta ga yana tsayawa da wata ko zai auro wata, to, sunan abinda take yi shine hassada ga 'yar'uwarta. 

A riwaya ta biyu kuma an nuna mana ne illar mace ace tana da maza biyu, domin idan hakan ta kasance za a sami tabarbarewar zuriya saboda idan aka tashi auren 'yar data haifa ba za a san wanene babanta ba daga cikin mazaje biyun. Shi kuwa namiji duk 'ya'yan ta matansa hudu (4) suka haifa komai yawansu za a jingina su ne gare shi, kenan za a sami tsarkin zuriya da mutunci ga wadannan 'ya'ya. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.

       (08137925034)

27TH MARCH, 2024/ 17TH RAMADAN, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post