🇳🇬 _ma'asumah_ _Nigerian_ . _News_ _updater_ _tare_ _da_ _wakilinsu_ *Real* *umary* *commissioner* *azare*
*WANKA* : mustahabbi ne yin wanka a Daren, Amma shi wankan Daaren lailatul kadri ya Dan bambanta da na sauran dararen Ramadan, domin an fi son yin sa ne bayan faduwar Rana, ta yadda za a yi sallah magriba da isha'i da wankan Na'am ba laifi ga Wanda Bai samu damar Yi a lokacin ba, ya yi a cikin Daren.
*SADAKA* : Ana son yin sadaka a Daren, domin tana tunkudewa Mai yi bala'o'in shekara, kuma tana kusanta mutum ga Allah ta'ala.
*ZIYARA* : A Ana son ziyarar Imam Hussain (AS) a wannan dare, domin ya zo a hadisi cewa, A Daren lailatul kadri, Mai kira yakan yi kira daga karkashin Al-Arshi a Saman bakwai, ya ce Hakika Allah ya yi gafarta ga duk Wanda ya ziyarci Hussaini(AS)" (mafatihu 347).
*TAWASSULI* : A wannan dare ana yin muhimmiyar Addu'ar Nan ta tawassuli da Alkur'ani, duba ' mafateehul-jinan' shafi na 346, ko 'Dhiya'us-saliheen' shafi na77, doganin yadda ake yi.
*JAUSHAN* : A na son karanta muhimmiyar addu'ar Nan Mai kaifi da tasiri wacce ke dauke da sunayen (Allah Dubu) wato 'Du'a'u jaushanil kabeer' a wannan dare domin duk abin da mutum ya Roki Allah, take zai biya masa.
*ISTIGFARI* *DA* *SALATI* : A wannan dare ana son yawaita yin Istigfari da salatin Annabi(S), an ruwaito cewa, Mafi karanci shi ne mutum ya yi Istigfari 100 da salatim Annabi 100 a daren. Sannan mustahabbi ne tsinewa makasan imam Ali (AS) sau 100 a Daren, ta hanyar fadin , Allahummal'an katalata Ameeril muminin"
*ADDU'A* : A Akwai addu'o'i jingim da ake karantawa a wannan dare Mai albarka, akwai masu tsawo akwai Kuma gajeru, Mai bukata sai ya koma ga littattafan addu'o'i irin su mafateehu, Dhiya:u, ikbal, Baladul Ameen da sauransu.
*MULAHAZA* : Idan dare ya yi was mutum kadan, ko lokacin ya kure masa Bai kammala ayyukan Daren ba, to akwai dama a gare shi ya yi sauran ayyukan da suka rage a yinin, domin ya zo a ruwa cewa , yinin lailatul-kadri tamkar darenta ne a falala.
*©REAL* *UMARY* *COMMISSIONER* *AZARE*
28/03/2024