SOYAYYAR AHLIL BAITY (A.S )

 


   Soyayyar Ahlil-baity (A.S) wajibi ne akan kowa, indai ka yarda da Manzon Allah (S.A.W.W) a matsayin shugaba kuma jagora a komai to dole ka yarda da Ahli-Baitin sa. (Imamai Sha biyu 12) a matsayin jagororin da Ya bar mana muyi riƙo da su.


 Soyayyar Ahlil-baity tukuci ne ga Annabinmu, duk masoyin Annabi na gaskiya dole ya Zama masoyin iyalan gidansa.

Kuma 'yan uwa mu sani fa duk Wanda ya so Ahlil-baity Annabi ya sosu. Duk Wanda yaƙi Ahlil-baity to Annabi yaƙi Kuma masoyin Annabi masoyin Allah ne, maƙiyin Annabi maƙiyin Allah ne.


Soyayyar Ahlil-baity biyayya ce ga Allah da Manzon Allah, 

Soyayyar Ahlil-baity tukuci ne ga manzon Allah. Soyayyar Ahlil-baity Haske ne me yaye munafinci, Soyayyar Ahlil-baity babban nasara ce  babban ni'ima ce kuma babban rabo ne.


 Soyayyar Ahlil-baity itace sama da komai, To shin in bamu so su ba munyi musu biyayya ba wa zamu riƙe su kaimu zuwa ga miƙaƙƙiyar hanyar gaskiya, wa Kama su Mana iso zuwa ga Annabinmu, wa zamu riƙe mu tsira, in banda tsarkakku Ahlin me girma da ƙasai ta 


Ilahi ya datar da mu a soyayyar Ahlil-Baitin Shugabanmu, ya ƙara ma iyayenmu lafiya da Nisan  kwana. Ya biya ma malamanmu buƙatun su na Alkhairi

Ilahi Bihakki Sahibuz zaman.


_Kauthar Muhammad Auwal Akeelah ✍️

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post