Shin da akwai wani abu da Kwakwalwa ko gangar jiki suke buqata bayan sun yi la'asar (ma'ana gajiya) baya ga hutu ?

 



Wani abin daure kai shi ne, yadda mutum yake manta cewa gangar jikinsa na da hakki a Kansa. Hakika jikimmu na bukatar hutu a kan Kari. Mafi yawammu mun mayar da kammu tamkar agogo ko wadansu na'urori. Ba mu yarda da mu huta ba, musamman a kan duk wani aikin da zai kawo mana kudi. Wadansu kuma sukan yi amfani da kwayoyi domin samar wa jikinsu kuzari, amma mu sani irin wadannan kwayoyi sukan yi wa gangar jiki illa. Sau tari sukan bata lafiyar Kwakwalwa, don Mun ga mutanen da suka susuce sakamakon amfani da kwayoyi


Wadansu kuma irin wadannan kwayoyi sun zamar musu jiki,  Za ka tarar ko da yaushe aiki ya taso musu komai  kankantarsa, sai sun yi amfani da irin wadannan kwayoyi sannan za su iya yinsa. 'Dan'adam na bukatar hutu domin samun damar aiwatar da wadansu ayyukansa na gaba. Idan ka samu hutu, to lallai Kwakwalwarka za ta huta, wanda kuma hakan kan sa gabban jiki su huta. 


Wannan hutu da ka yi, zai ba wa kwakwalwa damar sabunta tunane-tunanen da take yi, ka ji kana sha'awar aikata wadansu ayyuka. Mutane da dama sun dimauta da aikin da ke gabansu, har ma wannan dimauta ta sa rashin cigaba kan wannan aiki. Zuciya ce ke sarrafa gangar jikin 'Dan'adam wajen sa kaunar duk abin da ya sa a gaba.


Idan zuciyarmu ba ta kaunar aikin da muka sa a gaba, to sai gangar jikimmu ta nuna, ta hanyar kasala da ganin aikin mai wuya ne ko mai kankantarsa. Amma da zarar zuciya na sha'awar wannan aiki, komai yawansa. Sai ka ga cikin gaggawa jiki ya karba. Mu sani idan zuciyarmu ta gaji sakamakon rashin isasshen hutu daga gare mu, sai ta takura, har hakan ya sa mu daina jin dadin aiki da muke yi. Wannan na nuni da cewa idan zuciya ta takura, gangar jiki sai ta samu wannan sako, ka tarar cewa an tsinci kai cikin kasala.


__Zamu cigaba a rubutu na gaba..✍️


           Fatima Adamu Tinja.📝

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post