MUZAHARAR 12 DISAMBA A GARIN AZARE DAKE JAHAR BAUCHI
Yau juma'a, 15 ga Disamba, 2023 yan uwan musulmai Almajiran sayyid Ibraheem Zakzaky (H), sun ka gudanar da muzahara tinawa waki'ar buhari da ta faru yau shekara 8 da ta'addanci Buhari a ranar 12/13/14 ga Disamba, 2015 a garin Zaria.
Cincirendon ƴan uwa maza da mata yara da manya almajiran Shaikh Zakzaky (H) suka fito don tunawa ta'addanci da Buhari da El-Rufai, Burtai sukayi a garin Zaria kan Shaikh Zakzaky da almajiransa.
Muzaharar wacce ta fara gudana misalin karfe 2:40pm na yau juma'a An fara muzaharar ne a babbar masallacin juma'a na garin Azare ana tafe ana rera wakokin tinawa da abin da ya faru da yan uwa musulmi shekaru 8 a birnin Zaria jihar Kaduna, Kaduna.
. Alhamdulillah anyi muzaharar lafiya an tashi lafiya, ga wasu kadan daga yadda muzaharar ta gudana cikin hotun.
MEDIA FORUM AZARE
15/December/2023