MUZAHARAR 12 DISAMBA A ABUJA BIRNIN TARAYYAR NAJERIYA

 MUZAHARAR 12 DISAMBA A ABUJA BIRNIN TARAYYAR NAJERIYA



Yau Laraba, 13 ga Disamba, 2023 harkar musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar da muzahara tinawa da shekara 8 da ta'addanci Buhari a ranar 12/13/14 ga Disamba, 2015 a garin Zaria.


Cincirendon ƴan uwa maza da mata ne almajiran Shaikh Zakzaky (H) suka fito kan titin Herbert Macaulay, dauke da hotuna da rubuce-rubucen dake dauke da sakon bayyana irin ta'addanci da Buhari da El-Rufai, Burtai sukayi a garin Zaria kan Shaikh Zakzaky da almajiransa. 


Muzaharar wacce ta fara gudana misalin karfe 2 na ranar yau Laraba, daga babbar kasuwar Wuse Market zuwa gadan Bega. Masu muzaharar tafe suke suna rera wakokin tinawa da abin da ya faru da yan uwa musulmi shekaru 8 a birnin Zaria jihar Kaduna, Kaduna. 


Yau itace rana ta Biyu da fara taron makon tinawa da kisan kiyashin Zaria da ke gudana a Abuja karo na 8. Alhamdulillah anyi muzaharar lafiya an tashi lafiya, ga wasu kadan daga yadda muzaharar ta gudana cikin hotun.


-Asperger

13/December/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post