MATSAYIN AURE A MUSLIMCI !!! (5): SIFFAR MATAN DA YA KAMATA A NISANTA YAYIN AURE

 


Kamar yadda aka kwadaitar damu irin matan da ya kamata mu aura don jin dadin rayuwarmu ta duniya da lahira hakama aka gargade mu da nisantar wasu mata wajen aure.

Su wadannan mata babu wata natijar da ake samu  ta hanyar auren su, sai dai fitina, tashin hankali da rashin nutsuwa tare dasu. 

Manzon Allah (S. A. W. W) ya siffanto mana irin wadannan mata wadanda yace mu nisance su da nufin aure. Za mu iya ganinsu cikin wadannan misalai biyu daga hadisai biyu masu zuwa :

👇

24957- 1-[1] مُحَمَّدُ بْنُ يَعْقُوبَ عَنْ عِدَّةٍ مِنْ أَصْحَابِنَا عَنْ سَهْلِ بْنِ زِيَادٍ وَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدٍ وَ عَنْ عَلِيِّ بْنِ إِبْرَاهِيمَ عَنْ أَبِيهِ جَمِيعاً عَنِ ابْنِ مَحْبُوبٍ عَنْ عَلِيِّ بْنِ رِئَابٍ عَنْ أَبِي حَمْزَةَ عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ سَمِعْتُهُ يَقُولُ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ أَ لَا أُخْبِرُكُمْ بِشِرَارِ نِسَائِكُمُ الذَّلِيلَةُ فِي أَهْلِهَا الْعَزِيزَةُ مَعَ بَعْلِهَا الْعَقِيمُ الْحَقُودُ الَّتِي لَا تَتَوَرَّعُ مِنْ قَبِيحٍ الْمُتَبَرِّجَةُ إِذَا غَابَ عَنْهَا بَعْلُهَا الْحَصَانُ مَعَهُ إِذَا حَضَرَ لَا تَسْمَعُ قَوْلَهُ وَ لَا تُطِيعُ أَمْرَهُ وَ إِذَا خَلَا بِهَا بَعْلُهَا تَمَنَّعَتْ مِنْهُ كَمَا تَمَنَّعُ الصَّعْبَةُ عِنْدَ رُكُوبِهَا وَ لَا تَقْبَلُ مِنْهُ عُذْراً وَ لَا تَغْفِرُ لَهُ ذَنْباً."

Daga Muhammad Bn Ya'aquba, daga Iddatin daga cikin Sahabbanmu, daga Sahal Bn Ziyaad, kuma daga Muhammad Bn Yahya, daga Ahmad Bn Muhammad, kuma daga Aliyu Bn Ibrahim daga babansa gaba daya daga Ibn Mahbuub, daga Aliyu Bn Ri'ab, daga baban Hamzata daga Jabir Bn Abdullahi (R. A) yace : Na ji shi yana cewa Manzon Allah (S. A. W. W) yace :

" ASHE BANA BA KU LABARI GAME DA SHARRIN MATAYENKU BA  ? ITA CE QASQANTACCIYA CIKIN IYALINTA, MABUWAYIYA (mai Izzah)TARE DA MIJINTA MARAR HAIHUWA,  WALAQANTACCIYA WACCE BA TA KAWAR DA KAI DAGA MUMMUNA, KUMA MAI YIN TABARRUJI (caba ado na jan hankali) YAYIN DA MIJINTA BA YA NAN. MAI KATANGE KANTA TARE DASHI YAYIN DA YAKE NAN, BA TA JIN MAGANARSA KUMA BA TA BIYAYYA GA UMARNINSA. KUMA YAYIN DA YA KEBE DA ITA (don biyan buqatursa) SAI TA HANA SHI (kanta) KAMAR DAI YADDA SA'IBA (dabbar da ake tsare ta mai alfarma wacce ba a dora mata kaya kuma ba a hawanta)  KE QIN YARDA YAYIN HAWANTA, KUMA BA TA KARBAR UZURI DAGA GARE SHI KUMA BA TA GAFARTA MASA ZUNUBANSA (wadanda yayi mata). "

الكافي 5- 325- 1، و أورد صدره في الحديث 2 من الباب 6 من هذه الأبواب.

Lalle ana samun irin wannan mace cikin mata kuma ana iya fahimtarsu daga waje tun ka fin ayi aure, saboda haka a nisanci auren irinsu. 

Wata riwaya ta gaba kuma tana cewa :

24964- 8-[15] وَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عُمَرَ بْنِ عَلِيٍّ الْبَصْرِيِّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ الْحَسَنِ بْنِ بُنْدَارَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يُوسُفَ الطُّوسِيِّ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَلِيِّ بْنِ‏ حشرم [خَشْرَمٍ‏ عَنِ الْفَضْلِ بْنِ مُوسَى عَنْ أَبِي حَنِيفَةَ النُّعْمَانِ بْنِ ثَابِتٍ عَنْ حَمَّادِ بْنِ أَبِي سُلَيْمَانَ عَنْ إِبْرَاهِيمَ النَّخَعِيِّ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْن عُتَيْبَةَ عَنْ زَيْدِ بْنِ ثَابِتٍ قَالَ: قَالَ لِي رَسُولُ اللَّهِ ص يَا زَيْدُ تَزَوَّجْتَ قُلْتُ لَا قَالَ تَزَوَّجْ تَسْتَعِفَّ مَعَ عِفَّتِكَ وَ لَا تَزَوَّجَنَّ خَمْساً قَالَ زَيْدٌ مَنْ هُنَّ قَالَ لَا تَزَوَّجَنَّ شَهْبَرَةً وَ لَا لَهْبَرَةً وَ لَا نَهْبَرَةً وَ لَا هَيْدَرَةً وَ لَا لَفُوتاً قَالَ زَيْدٌ مَا عَرَفْتُ مِمَّا قُلْتَ شَيْئاً (قَالَ) أَ لَسْتُمْ عَرَباً أَمَّا الشَّهْبَرَةُ فَالزَّرْقَاءُ الْبَذِيَّةُ وَ أَمَّا اللَّهْبَرَةُ فَالطَّوِيلَةُ الْمَهْزُولَةُ وَ أَمَّا النَّهْبَرَةُ فَالْقَصِيرَةُ الدَّمِيمَةُ وَ أَمَّا الْهَيْدَرَةُ فَالْعَجُوزُ الْمُدْبِرَةُ وَ أَمَّا اللَّفُوتُ فَذَاتُ الْوَلَدِ مِنْ غَيْرِكَ."

Daga Muhammad Bn Umara Bn Aliyu Al-Basriy, daga Aliyu Bn Hassan Bn Bundaara, daga Muhammad Bn Yusufa Al-'Dusiyyi, daga babansa daga Aliyu Bn Hashrami/Khashrami, daga Fadhal Bn Musa, daga Abu Hanifata An-Nu'umaan Bn Thaabit, daga Hammad Bn Abiy Sulaimana, daga Ibrahim An-Nuka'i, daga Abdullahi Bn Utaibata, daga Zaid Bn Thaabit yace : Manzon Allah (S. A. W. W) ya ce min :

" YAA ZAID  ! KA YI AURE  ?" Nace : " A'a  ."

Yace : " KAYI AURE ZA KA KAME TARE DA KAMEWARKA, KUMA KADA KA AURI :-

(i) - SHAHBATU , 

(ii)- DA LAHBARATU , 

(iii)- DA NAHBARATU , 

(i)- DA HAIDARATU , 

(v )- DA KUMA LAFUUTU  ."

Sai Zaid yace : " Ban san wani abu daga (ma'anar) abinda ka fada ba. " Yace (S. A. W. W) :

" KAI BA BALARABE BANE  ? AMMA (ma'anar) :-

(1)- SHAHBARATU ITA CE MACE MAI CI DA YAWA (gluton).

(2)- LAHABARATU ITA CE MACE MAI YAWAN QIBA (too fat).

(3)- NAHBARATU ITA CE MACE WACCE KE 'DAGA SAUTI SOSAI IN TANA MAGANA.

(4)- HAIDARATU ITA CE MACE TSOHUWA WACCE  BA ZA AYI SHA'AWARTA BA. 

(5)- LAFUUTU ITA CE MACE MAI 'YA'YA A WANI GIDA (wadanda ba 'ya'yanka bane). 

الخصال 316- 98.

           ABIN LURA ANAN 

(1)- Auren mace mai ci da yawa ba ta haquri da abu qanqani, kuma za ta raina maka in har ba ka da wadata. 

(2)- Mace mai yawan qiba babu abin sha'awa tare da ita (sai dai in iliminta ko kyawawan halayenta) , kuma abubuwa da yawa za su iya kubuce mata domin ba za ta iya ba saboda kasala.

(3)- Ita kuwa mace mai daga sauti yayin magana ta zama tamkar Jaki ne wanda Allah ya hane mu da siffantuwa dashi.

(4)- Ita kuwa tsohuwar mace akwai ta makirci kuma ana samun qarancin sha'awa daga gare ta. Idan kuwa aka ce ba mace ba ta da sha'awa ba za ka sami biyan buqatarka daga gare ta ba, kuma kaima ba za ka riqa sha'awarta kamar yadda za kayi sha'awar yarinya ba. Wannan dalili yasa maqiya suka qirqiri cewa Nana Khadijah tsohuwa ce, kuma A'ishatu qaramar yarinya ce. 

(5)- Ita kuwa mace mai 'ya'ya a wani gida hankalinta ba ya tataruwa guri guda, wani lokaci ma sai kaga ana samun sabani tsakaninka da ita sakamakon 'ya'yanta na wani gida. 

MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


            (08137925034)


3rd December, 2023/  20th Jimada-Ulah, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post