KOWA SAI YA YI IQIRARI DA WILAYAR ALI (A. S) KA FIN MUTUWARSA !!!



MATSAYIN IMAM ALI TAMKAR MATSAYIN ANNABI ISAH (A. S) YAKE 

Imam Ali (A. S) cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) tamkar matsayin Annabi Isah (A. S) ne cikin Banu Isra'ila. Abubuwan da suka faru na Mu'ujizozi ko Karamomin Isah Al-Masihu (A. S) sun bayana ga Imam Ali (A. S). 

Yadda Isah Almasihu (A. S) ya tayar da matattu haka Imam Ali (A. S) ya tayar da Gawa kuma tayi magana dashi. Kamar yadda Nasara suka fifita Isah Almasihu (A. S) suka ba shi matsayi na Allantaka hakama wasu daga cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) suka daukaka Aliyu (A. S) zuwa wani matsayi na Allantaka. 

Imam Ali (A. S) na cewa :

" MUTANE BIYU ZA SU HALAKA SABODA NI. 

(i) - WANDA YA KAI NI MATSAYIN DA BAN KAI BA. 

(ii) - WANDA YA TSANANTA QIYAYYA A GARE NI. "

Wanda ya kai shi matsayin da bai kai ba shine wanda yace shi Annabi ne ko wanda yace shi Allah ne. 

Wanda ya tsananta qiyayyarsa gare shi kuwa wanda ya qi miqa Wilayarsa gare shi da wadanda suka yaqe shi.

To, duk wanda ya tsananta qiyayya gare shi ko yaqi miqa Wilayarsa gare shi dole sai ya miqa kafin mutuwarsa, sai dai ace ya miqata ne a lokacin da ba za ta amfane shi ba. 

Dangane da Annabi Isah Almasihu (A. S) Allah (T) na cewa :

👇

{وَإِنْ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ إِلَّا لَيُؤْمِنَنَّ بِهِ قَبْلَ مَوْتِهِ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكُونُ عَلَيْهِمْ شَهِيدًا (159)} ﴾ 

" KUMA BABU (wani) DAGA CIKIN AHLUL-KITAAB FACE SAI YA YI IMANI DASHI KA FIN MUTUWARSA, KUMA RANAR ALQIYAMA ZAI KASANCE MAI SHAIDA A KANSA. "

                  (NISA'I :159)

Ma'ana duk wani mai cewa Annabi Isah (A. S) Allah sai ya dawo ya yi imani da cewa shi ba Allah bane AnnabinSa ne kuma bawa daga cikin bayinSa, hakan kuwa zai faru ne ga masu cewa shi Allah ne ko dan Allah kafin (A. S) ya koma zuwa ga Mahalicinsa. 

Ya zo cikin riwaya kamar haka :

                          (1)

الرسول (صلى الله عليه وآله)- يَا عَلِيُّ (عليه السلام) إِنَّ فِيكَ مَثَلًا مِنْ عِيسَي‌ابْنِ‌مَرْيَمَ (عليه السلام) قَالَ اللَّهُ تَعَالَى وَ إِنْ مِنْ أَهْلِ الْكِتابِ إِلَّا لَيُؤْمِنَنَّ بِهِ قَبْلَ مَوْتِهِ وَ يَوْمَ الْقِيامَةِ يَكُونُ عَلَىْهِمْ شَهِيداً يَا عَلِيُّ (عليه السلام) إِنَّهُ لَا يَمُوتُ رَجُلٌ يَفْتَرِي عَلَى عِيسَي‌ابْنِ‌مَرْيَمَ (عليه السلام) حَتَّي يُؤْمِنَ بِهِ قَبْلَ مَوْتِهِ وَ يَقُولَ فِيهِ الْحَقَّ حَيْثُ لَا يَنْفَعُهُ ذَلِكَ شَيْئاً وَ إِنَّكَ عَلَى مَثَلِهِ لَا يَمُوتُ عَدُوُّكَ حَتَّي يَرَاكَ عِنْدَ الْمَوْتِ فَتَكُونَ عَلَىْهِ غَيْظاً وَ حُزْناً حَتَّي يُقِرَّ بِالْحَقِّ مِنْ أَمْرِكَ وَ يَقُولَ فِيكَ الْحَقَّ وَ يُقِرَّ بِوَلَايَتِكَ حَيْثُ لَا يَنْفَعُهُ ذَلِكَ شَيْئاً وَ أَمَّا وَلِيُّكَ فَإِنَّهُ يَرَاكَ عِنْدَ الْمَوْتِ فَتَكُونُ لَهُ شَفِيعاً وَ مُبَشِّراً وَ قُرَّةَ عَيْنٍ."

Manzon Allah (S.A.W.W) ya ce :

" YAA ALIYU ! LALLE CIKINKA AKWAI MISALI DAGA ISAH IBN MARYAMA (A. S), ALLAH MADAUKAKI YA CE : " KUMA BABU DAGA AHLUL-KITAABI FACE YA YI IMANI DASHI KA FIN MUTUWARSA, KUMA A RANAR ALQIYA ZAI KASANCE SHAIDA A KANSU. "

YAA ALIYU ! LALLE BABU WANI DAGA CIKIN WADANDA SUKA QIRQIRI QARYA GA ISAH (cewa shi Allah né) WANDA ZAI MUTU FA CE YA YI IMANI DASHI KA FIN MUTUWARSA (A. S), KUMA YA FADI GASKIYA A KANSA (cewa lalle shi fa ya san cewa shi Annabi ne) A LOKACIN DA HAKAN BA ZAI AMFANAR DASHI WANI ABU BA. 

KUMA KAI KANA AKAN MISALINSA, BABU WANDA ZAI MUTU DAGA MAQIYANKA FA CE SAI YA GANKA YAYIN MUTUWA, BAQIN CIKI DA BACIN RAI YA KASANCE GARE SHI, HAR SAI YA YI IQIRARI DA GASKIYA DAGA AL'AMARINKA, KUMA YA FADI GASKIYA A KANKA, KUMA YAYI IQIRARI DA WILAYARKA A LOKACIN DA HAKAN BA ZAI AMFANAR DASHI DA WANI ABU BA. 

AMMA SHI MASOYINKA, TO, SHI YANA GANINKA YAYIN MUTUWA, SAI (Wilayarsa gare ka) TA KASANCE MAI CETO GARE SHI KUMA MAI BADA BUSHARA (Albishir) KUMA SANYIN IDANUWA (gare shi). "

المصدر : بحارالأنوار، ج6، ص194/

 فرات الكوفي، ص116 

- تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص512

                       (2)

الصادق (عليه السلام)- لَمَّا نَزَلَتْ هَذِهِ الْآيَةُ وَ إِنْ مِنْ أَهْلِ الْكِتابِ إِلَّا لَيُؤْمِنَنَّ بِهِ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ (صلى الله عليه و آله) لَا يَرُدُّ أَحَدٌ عَلَى عِيسَي‌ابْنِ‌مَرْيَمَ (عليه السلام) مَا جَاءَ بِهِ فِيهِ إِلَّا كَانَ كَافِراً وَ لَا يَرُدُّ عَلَى عَلِيِّ‌بْنِ أَبِي‌طَالِبٍ (عليه السلام) أَحَدٌ مَا قَالَ فِيهِ النَّبِيُّ (صلى الله عليه و آله) إِلَّا كَافِرٌ.

Daga Imam Sadiq (A. S), yayin da wannan aya ta sauka :

" KUMA BABU (wani) DAGA AHLUL-KITAABI FA CÊ YA YI IMANI DASHI... " Yace : Manzon Allah (S. A.W.W) ya ce :

" BABU WANDA ZAI YI JAYAYYA DA ISAH 'DAN MARYAMA (A. S) CIKIN ABINDA YAZO DASHI FACE YA KASANCE KAFIRI. KUMA BABU WANDA ZAI YI JAYAYYA DA ALI (A. S) GAME DA ABINDA ANNABI (S. A. W. W) YA FADA A KANSA FACE KAFIRI. "

المصدر : وسائل الشيعةًْ، ج28، ص345/ فرات الكوفي، ص115/

 بحارالأنوار، ج6، ص188/ العياشي، ج1، ص283/


 البرهان - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص512

Ya Allah ka sanya mu cikin masoya Imam Ali (A. S) na haqiqa masu miqa Wilaya ta gaskiya gare shi.

MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES

Daga wakilinmu na Bauchi zone. 

✍🏽Ado Isah Guda.

              (08137925034)

1st December, 2023/ 18th Jimada-Ulah, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post