Wawanci ko wauta aiki ne na zargi wanda bai kamata ace an same shi tare da mutum ba. Wani kan iya zama dabi'a ce wacce aka halicce shi kanka, wani kuma ya kanyi ne amma yakan iya canzawa. Shi kuwa wawanci na dabi'a/wauta ba ya canzawa, idan Allah ya hada ka zama da irinsu sai dai haquri.
Ya zo cikin riwaya daga Imam Ali (A. S) inda yake cewa :
👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" الْحُمْقُ دَاءٌ لَا يُدَاوَى وَمَرَضٌ لَا يَبْرَأُ."
" WAWANCI CUTA CE DA BA A YI MATA MAGANI, KUMA CIWO NE WANDA BA YA WARKEWA. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Darasin dake cikin wannan hadisi shine, shi wawanci/wauta cuta ce wacce ba a yi mata magani, kuma ciwo ne wanda in kace za kayi masa magani ma ba zai warke ba. Saboda haka in Allah ya hada ka zama da irin wadannan mutane sai dai haquri da dabi'unsu, amma dai ba abune wanda za ka iya raba su dashi ba.
Cikin riwayar dake tafe kuma ya siffanta mana yadda ake iya gane mutum shi wawa ne kamar yadda za muga siffofinsa.
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" تُعْرَفُ حَمَاقَةُ الرَّجُلِ فِي ثَلَاثٍ فِي كَلَامِهِ فِيمَا لَا يَعْنِيهِ وَجَوَابِهِ عَمَّا لَا يُسْأَلُ عَنْهُ وَتَهَوُّرِهِ فِي الْأُمُورِ."
" ANA GANE WAWANCIN MUTUM NE CIKIN ABU UKU.
(1)- CIKIN MAGANARSA AKAN ABINDA BAI SHAFE SHI BA.
(2)- DA BAYAR DA AMSARSA KAN ABINDA BA A TAMBAYE SHI BA.
(3)- DA YIN SHIGEGENSA CIKIN AL'AMRA. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Duk wanda ka gan shi cikin wadannan siffofi uku to, sunansa wawa mai wauta.
Bai kamata ga mai hankali nutsatse ya zama yana sa kansa cikin abinda bai shafe shi ba, ko kuma yaji wani na tambayar wasu wani abu shi kuma sai yayi zarar ya bada amsa bisa hujjar ya sani, ko kuma yaga mutane na yin al'amransu sai ya shiga cikinsu ba tare da an neme shi ba.
Tabbas, mai wannan dabi'a sunansa wawa komai karatunsa. Sannan ba zai taba yin mutunci cikin mutane ba, domin tsoma kansa cikin abubuwan da basu shafe shi ba zai sa a riqa jin haushinsa.
Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa :
" YANA DAGA CIKIN CIKAR ADDININ MUTUM BARIN ABINDA BAI SHAFE SHI BA. "
Sai dai kuma wani uzuri da za a iya yiwa mutum shine, idan yaga ana zaluntar wani ko ana qoqarin a zalunce shi sai yayi magan, to, bai yi laifi ba domin ma ya aikata abinda Allah ne ke so.
MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th December, 2023/ 21st Jimada-Ulah, 1445.
Tags:
Daga marubuta