Daga irin wannan safiyar bamu qara waya ba
Saboda Ina zaune a harabar gida kan carpet nayo alwala na dauko mafatihu wallahi nasashi gaba da carbi na kasa cewa komi na kurawa mafatihun ido zuciyata nata bugawa
Saina daga waya naita kiransa baya shiga inya shiga bazai daga ba Ina cikin kuka sai naga text dinsa na cewa 'Zan kiraki'💔
Wallahi har yau Bai kirani na😭😭😭
Zanta Jira bazan gaji ba😢💔,
Can sai Qawata dake Zaria ta kirani (Maman jidda) matar brother Dan bara'a yanzu
Tana kuka tana cemin M Turi yayi Shahada
Innalillahi wa inna ilahirraji'un 😭
Na fashe da kuka, kawai saina tashi na rufe gidan na nufi cikin gida (Main house dinsu) kasancewar bamuda Nisa
Wallahi da naje kasa shiga nayi saboda bansan me zan cewa Hajiya ba kasancewar har lokacin ban Kara ma waya da Abbansu ba😭💔
Ina nan zaure Ina kuka ashe wata tazo ta ganni taje ta Kira Hajiyan tace ga wata can kamar Amaryar Iro, shine tazo ta shiga Dani ciki, Already ta Riga tasan meke faruwa
Tayita bani Baki cikin tausayawa (Hajiya Allah ya jikanki wallahi nayi rashin Uwa 😭).
Nan muka cigaba da zaman Jiran tsammani......