BAYAN KAMMALA PROGRAM DIN TUNAWA DA WAKI'AR BUHARI, AN CIGABA DA MUZAHARA A GARIN AZARE

 BAYAN KAMMALA PROGRAM DIN TUNAWA DA WAKI'AR BUHARI, AN CIGABA DA MUZAHARA A GARIN AZARE



Bayan An tashi daga Program din tunawa da Waki'ar Buhari wanda Harisawan Azare unit, suka shirya yanzu haka kuma Muzahara ce ke cigaba da gudana cikin salo tare da bayyana ma al'umma cewa bamu manta ba, kuma bazamu yafe ba da kisan kiyashin da Buhari da Buratai da Elrufa'i sukayi akan Almajiran Shaikh Zakzaky (H) a garin Zaria dake jihar Kaduna, wanda aka kwana Ukku ana harbin yan'uwa.


An fara Muzaharar ne daga fudiyya islamiyya Azare, ta biyo ta kan titin tshar dan Asabe zuwa yanzu haka anzo wajen Rufe Muzaharar ana daga Tutar Palestine. 


Bayan nan Shekh Aliyu dawud Abubakar wakilin yan na garin Azare yayi takaitaccen jawabin rufewa, sai akayi addu'a aka sallami yan'uwa baki daya. 


MEDIA FORUM AZARE

17/12/2023.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post