ADADIN LIMAMAN SHIRIYA DA SUNAYENSU
Babu wani qarni daga cikin qarnonin da suka gabata wanda ba zalunci ne ya fara damfaruwa a kansa ba, sai dai daga baya Allah kan tayar da bayinSa Manzanni (A. S) ko salihai wadanda suke kawar da wannan zalunci su shimfida adalci a madadinsa.
Kafin bayyanar Manzon Allah (S. A. W. W) kafirci ne da zalunci ke iko, sai Allah ya aiko da Manzon Rahma Muhammad (S. A. W. W) ya shafe wannan kafirci da zalunci.
Bayan wafatin Annabi (S. A. W. W) al'amra sun koma kamar na baya yadda ba abinda ya bari akayi riqo dasu ba, sai aka riqi bautar zuciya da Shaidan wadanda suka zama sune jagororin al'umma na wancan lokaci. A irin wannan yanayi ake tafiyar da al'amra, ana samun masu qoqarin kawo gyara kuma masu barna na cigaba da barnarsu.
ALQAWARIN ALLAH NE ZAI SHUGABANTAR DA MUMINAI A DORON QASA
٧٦٩٩/ «٦»- مُحَمَّدُ بْنُ الْعَبَّاسِ: عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ مُحَمَّدٍ، عَنْ مُعَلَّى بْنِ مُحَمَّدٍ، عَنِ الْوَشَّاءِ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ سِنَانٍ، قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ (عَلَيْهِ السَّلَامُ) عَنْ قَوْلِ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ: وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَ عَمِلُوا الصَّالِحاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِي الْأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ، قَالَ: «نَزَلَتْ فِي عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ، وَ الْأَئِمَّةِ مِنْ وُلْدِهِ (عَلَيْهِمُ السَّلَامُ)».
وَ لَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضى لَهُمْ وَ لَيُبَدِّلَنَّهُمْ مِنْ بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْناً، قَالَ: «عَنَى بِهِ ظُهُورَ الْقَائِمِ (عَلَيْهِ السَّلَامُ)».
An karbo daga Muhammad Bn Abbas, daga Hussaini Bn Muhammad, daga Mu'allah Bn Muhammad daga Wassha'i, daga Abdullahi Bn Sinaan yace : " Na tambayi baban Abdullah (A. S) dangane da fadin Allah mai girma da daukaka :
" ALLAH YAYI ALQAWARI GA WADANDA SU KAYI IMANI DAGA CIKINKU DA WADANDA SU KAYI IMANI (cewa) ZAI SHUGABANTAR DASU CIKIN QASA KAMAR YADDA YA SHUGABANAR DA WADANDA KE GABANINSU. "
Yace : " TA SAUKA NE AKAN ALIYU BN ABU 'DALIB DA LIMAMAI DAGA 'YA'YANSA (A. S). "
" KUMA ZAI TABBATAR MUSU DA ADDININSU WANDA YA YARDAR MUSU, KUMA ZAI CANZA MUSU DA AMINCI BAYAN TSORO. "
Yace : " ABIN NUFI DASHI SHINE BAYYANAR QA'EEM (A.S)."
٧٧٠٠/ «٧»- ابْنُ بَابَوَيْهِ، قَالَ: حَدَّثَنَا أَبُو الْمُفَضَّلِ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ الشَّيْبَانِيُّ (رَحِمَهُ اللَّهُ)، قَالَ:
حَدَّثَنَا أَبُو مُزَاحِمٍ مُوسَى بْنُ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ يَحْيَى بْنِ خَاقَانَ الْمُقْرِئُ بِبَغْدَادَ، قَالَ: حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرٍ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ إِبْرَاهِيمَ الشَّافِعِيُّ، قَالَ: حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ حَمَّادِ بْنِ مَاهَانَ الدَّبَّاغُ أَبُو جَعْفَرٍ، قَالَ: حَدَّثَنَا عِيسَى بْنُ إِبْرَاهِيمَ، قَالَ:
حَدَّثَنَا الْحَارِثُ بْنُ نَبْهَانَ، قَالَ: حَدَّثَنَا عُتْبَةُ بْنُ يَقْظَانَ، عَنْ أَبِي سَعِيدٍ، عَنْ مَكْحُولٍ، عَنْ وَاثِلَةَ بْنِ الْأَسْقَعِ بْنِ أَبِي قِرْصَافَةَ «٢»، عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ الْأَنْصَارِيِّ، قَالَ: دَخَلَ جَنْدَلُ بْنُ جُنَادَةَ الْيَهُودِيُّ مِنْ خَيْبَرَ عَلَى رَسُولِ اللَّهِ (صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ)، فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ، أَخْبِرْنِي عَمَّا لَيْسَ لِلَّهِ، وَ عَمَّا لَيْسَ عِنْدَ اللَّهِ، وَ عَمَّا لَا يَعْمَلُهُ اللَّهُ. فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ (صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ): «أَمَّا مَا لَيْسَ لِلَّهِ، فَلَيْسَ لِلَّهِ شَرِيكٌ، وَ أَمَّا مَا لَيْسَ عِنْدَ اللَّهِ، فَلَيْسَ عِنْدَ اللَّهِ ظُلْمٌ لِلْعِبَادِ، وَ أَمَّا مَا لَا يَعْلَمُهُ اللَّهُ، فَذَلِكَ قَوْلُكُمْ- يَا مَعْشَرَ الْيَهُودِ-: إِنَّ عُزَيْراً ابْنُ اللَّهِ، وَ اللَّهِ لَا يَعْلَمُ لَهُ وَلَداً». فَقَالَ جَنْدَلٌ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَ أَنَّكَ رَسُولُ اللَّهِ حَقّاً.
ثُمَّ قَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنِّي رَأَيْتُ الْبَارِحَةَ فِي النَّوْمِ مُوسَى بْنَ عِمْرَانَ (عَلَيْهِ السَّلَامُ)، فَقَالَ لِي: يَا جَنْدَلُ، أَسْلِمْ عَلَى يَدِ مُحَمَّدٍ (صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ)، وَ اسْتَمْسِكْ بِالْأَوْصِيَاءِ مِنْ بَعْدِهِ، فَقَدْ أَسْلَمْتُ، وَ رَزَقَنِيَ اللَّهُ ذَلِكَ، فَأَخْبِرْنِي بِالْأَوْصِيَاءِ بَعْدَكَ، لِأَتَمَسَّكَ بِهِمْ. فَقَالَ: «يَا جَنْدَلُ، أَوْصِيَائِي مِنْ بَعْدِي بِعَدَدِ نُقْبَاءِ بَنِي إِسْرَائِيلَ». فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّهُمْ كَانُوا اثْنَيْ عَشَرَ، هَكَذَا وَجَدْنَاهُمْ فِي التَّوْرَاةِ، قَالَ: «نَعَمْ، الْأَئِمَّةُ بَعْدِي اثْنَا عَشَرَ».
فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، كُلُّهُمْ فِي زَمَنٍ وَاحِدٍ؟ قَالَ: «لَا، وَ لَكِنْ خَلَفٌ بَعْدَ خَلَفٍ، وَ إِنَّكَ لَنْ تُدْرِكَ مِنْهُمْ إِلَّا ثَلَاثَةً».
Daga Ibn Mardawaihi yace : Baban Mufaddal Muhammad Bn Abdullahi Bn Abdul-Mudallib Al-Shaibaaniy (R. L) ya bamu labari yace :
Baban Murrata Musa Bn Abdullahi Bn Yahya Bn Khaaqaana Al-Muqriyyu ya bamu labari a Bagdaad yace : Abubakar Muhammad Bn Abdullahi Bn Ibrahim As-Shafi'i ya bamu labari yace : Muhammad Bn Hammaad Bn Maahaana Ad-Dayyaagu Baban Ja'afar ya bamu labari yace :
Isah Bn Ibrahim ya bamu labari yace : Harisu Bn Nabhaan ya ce, Utbatu Bn Yaqzaana ya bamu labari daga baban Sa'eed, daga Makhuul, daga Waathilata Bn Asqa'a Bn Abiy Qirsaafata, daga Jabir Bn Abdullahi Al-Ansari yace :
" Jandalu Bn Junadata Al-Yahudiyyu daga Khaibara ya shiga wajen Manzon Allah (S. A. W. W) sai yace : " Yaa Muhammad ! Ka bani labari game da abinda Allah ba shi dashi da kuma abinda babu shi tare da Allah, da kuma Abinda Allah bai san shi ba.
Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace :
" AMMA ABINDA ALLAH BA SHI DASHI SHINE BA SHI DA ABOKIN TARAYYA. KUMA ABINDA ALLAH BA SHI DASHI SHINE BABU ZALUNCI TARE DASHI GA BAYI. KUMA ABINDA ALLAH BAI SAN SHI BA SHINE FADINKU YAA KU TARON YAHUDAWA : " LALLE UZAIRU 'DAN ALLAH NE. " KUMA ALLAH BAI SAN YANA DA 'DA BA. "
Sai Jandaalu yace : " Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma kai Manzon Allah ne na gaskiya. "
Sa'an nan yace : " Yaa Ma'aikin Allah, lalle ni na ga Musa Bn Imrana (A. S) cikin baccina (mafarki), sai yace min :
" YAA JANDALU ! KA SALLAMA A HANNUN MUHAMMADU (S. A W. W) KUMA KAYI RIQO DA WASIYYAI A BAYANSA. "
To, haqiqa na sallama kuma Allah ya azurtani da haka. Ka bani labari game da wasiyyai a bayanka domin nayi riqo dasu. Sai (S. A.W.W) yace :
" YAA JANDALU ! WASIYYAI A BAYANA KAMAR ADADIN WAKILAN BANU ISRA'ILA SUKE. " Sai yace :
" Yaa Manzon Allah, sun kasance goma sha biyu (12) ne. Kamar haka muka same su cikin Attaura. " Yace :
" EH, LIMAMAI A BAYANA GOMA SHA BIYU (12) NE. "
Sai yace : " Yaa Ma'aikin Allah, dukkansu a zamani daya (1) suke ?" Yace :
" A'A, SAI DAI MASU MAYEWA NE BAYAN WASU SUN MAYE. KUMA KAI BA ZA KA RISKA DAGA GARE SU BA FACE UKU (3)."
قَالَ: فَسَمِّهِمْ لِي، يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَالَ: «نَعَمْ، إِنَّكَ تُدْرِكُ سَيِّدَ الْأَوْصِيَاءِ، وَ وَارِثَ الْأَنْبِيَاءِ، وَ أَبَا الْأَئِمَّةِ عَلِيَّ بْنَ أَبِي طَالِبٍ بَعْدِي، ثُمَّ ابْنَهُ الْحَسَنَ، ثُمَّ الْحُسَيْنَ، فَاسْتَمْسِكْ بِهِمْ مِنْ بَعْدِي، وَ لَا يَغُرَّنَّكَ جَهْلُ الْجَاهِلِينَ، فَإِذَا كَانَ وَقْتُ وِلَادَةِ ابْنِهِ عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ سَيِّدِ الْعَابِدِينَ، يَقْضِي اللَّهُ عَلَيْكَ، وَ يَكُونُ آخِرُ زَادِكَ مِنَ الدُّنْيَا شَرْبَةً مِنْ لَبَنٍ تَشْرَبُهُ».
فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، هَكَذَا وَجَدْتُ فِي التَّوْرَاةِ: إليا يقطو شَبَّراً وَ شَبِيراً، فَلَمْ أَعْرِفْ أَسْمَاءَهُمْ، فَكَمْ بَعْدَ الْحُسَيْنِ مِنَ الْأَوْصِيَاءِ، وَ مَا أَسَامِيهِمْ؟ فَقَالَ: «تِسْعَةٌ مِنْ صُلْبِ الْحُسَيْنِ، وَ الْمَهْدِيُّ مِنْهُمْ، فَإِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ الْحُسَيْنِ، قَامَ بِالْأَمْرِ مِنْ بَعْدِهِ عَلِيٌّ ابْنُهُ، وَ يُلَقَّبُ بِزَيْنِ الْعَابِدِينَ، فَإِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ عَلِيٍّ، قَامَ بِالْأَمْرِ مِنْ بَعْدِهِ مُحَمَّدٌ ابْنُهُ، وَ يُدْعَى بِالْبَاقِرِ، فَإِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ مُحَمَّدٍ قَامَ بِالْأَمْرِ بَعْدَهُ ابْنُهُ جَعْفَرٌ، يُدْعَى بِالصَّادِقِ، فَإِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ جَعْفَرٍ، قَامَ بِالْأَمْرِ مِنْ بَعْدِهِ ابْنُهُ مُوسَى، وَ يُدْعَى بِالْكَاظِمِ، ثُمَّ إِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ مُوسَى، قَامَ بِالْأَمْرِ مِنْ بَعْدِهِ عَلِيٌّ ابْنُهُ، يُدْعَى بِالرِّضَا، فَإِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ عَلِيٍّ، قَامَ بِالْأَمْرِ بَعْدَهُ مُحَمَّدٌ ابْنُهُ، يُدْعَى بِالزَّكِيِّ، فَإِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ مُحَمَّدٍ، قَامَ بِالْأَمْرِ بَعْدَهُ عَلِيٌّ ابْنُهُ، يُدْعَى بِالنَّقِيِّ، فَإِذَا انْقَضَتْ مُدَّةُ عَلِيٍّ، قَامَ بِالْأَمْرِ مِنْ بَعْدِهِ ابْنُهُ الْحَسَنُ، يُدْعَى بِالْأَمِينِ، ثُمَّ يَغِيبُ عَنْهُمْ إِمَامُهُمْ».
قَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، هُوَ الْحَسَنُ يَغِيبُ عَنْهُمْ؟ قَالَ: «لَا، وَ لَكِنِ ابْنُهُ الْحُجَّةُ».
Yace : " Ka ambata min su yaa Ma'aikin Allah. " Yace :
" NA'AM, LALLE KAI ZA KA RISKI SHUGABAN WASIYYAI KUMA MAGAJIN ANNABAWA, KUMA BABAN LIMAMAI ALIYU BN ABIY 'DALIB A BAYANA. SA'AN NAN 'DANSA HASSAN, SA'AN NAN HUSSAINI. KAYI RIQO DASU A BAYANA, KADA JAHILCIN JAHILAI YA RUDAR DA KAI, IDAN LOKACIN HAIHUWAR 'DANSA ALIYU BN HUSSAINI SHUGABAN MASU IBADA YAYI ALLAH ZAI YI HUKUNCI A KANKA. KUMA ZAI KASANCE QARSHEN GUZURINKA A DUNIYA SHA (drink) NE DAGA NONO WANDA ZA KA SHA. "
Sai yace :
" Yaa Ma'aikin Allah, kamar haka muka samu cikin Attaura : Ana kiransu SHABBARA DA SHABEERAN. Ban san sunayensu ba, wana ne wasiyyai a bayan Hussaini ? Kuma menene sunayensu ?" Sai yace :
" SU TARA NE DAGA TSATSON HUSSAINI, KUMA MAHDI NA DAGA CIKINSU. IDAN LOKACIN HUSSAINI YA QARE WANDA ZAI TSAYA DA AL'AMARI A BAYANSA SHINE ALIYU 'DANSA, ZA AYI MASA LAQABI DA ZAINUL-ABIDEEN. IDAN LOKACIN ALIYU YA QARE WANDA ZAI TSAYA DA AL'AMARINSA A BAYANSA SHINE MUHAMMAD 'DANSA, ANA KIRANSA DA BAQEER. IDAN LOKACIN MUHAMMAD YA QARE 'DANSA JA'AFAR NE ZAI TSAYA DA AL'AMARINSA, ANA KIRANSA DA SAADIQ. IDAN LIKACIN JA'AFAR YA QARE WANDA ZAI TSAYA DA AL'AMARINSA A BAYANSA SHINE 'DANSA MUSA, ANA KIRANSA DA KAAZEM. SA'AN NAN IDAN LOKACIN MUSA YA QARE WANDA ZAI TSAYA DA AL'AMARI A BAYANSA SHINE ALIYU 'DANSA, ANA KIRANSA DA RIDHAA. IDAN LOKACIN ALIYU YA QARE WANDA ZAI TSAYA DA AL'AMARI A BAYANSA SHINE 'DANSA MUHAMMAD, ANA KIRANSA DA AZZAKIYYU. IDAN LOKACIN MUHAMMAD YA QARE WANDA ZAI TSAYA DA AL'AMARI A BAYANSA SHINE 'DANSA ALIYU, ANA KIRANSA DA ANNAQIYYI. IDAN LOKACIN ALIYU YA QARE WANDA ZAI TSAYA DA AL'AMARI SHINE 'DANSA HASSAN, ANA KIRANSA DA AMEEN, SA'AN NAN LIMAMINSU ZAI FAKU.
Yace : " Yaa Ma'aikin Allah, shine Hassan wanda zai faku daga gare su ?" Yace :
" A'A, SAI DAI 'DANSA NE AL-HUJJA. "
قَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، فَمَا اسْمُهُ؟ قَالَ: «لَا يُسَمَّى حَتَّى يَظْهَرَ».
فَقَالَ: جَنْدَلُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَدْ وَجَدْنَا ذِكْرَهُمْ فِي التَّوْرَاةِ، وَ قَدْ بَشَّرَنَا مُوسَى بْنُ عِمْرَانَ بِكَ، وَ بِالْأَوْصِيَاءِ مِنْ ذُرِّيَّتِكَ.
ثُمَّ تَلَا رَسُولُ اللَّهِ (صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ): وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَ عَمِلُوا الصَّالِحاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِي الْأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِنْ قَبْلِهِمْ وَ لَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضى لَهُمْ وَ لَيُبَدِّلَنَّهُمْ مِنْ بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْناً فَقَالَ جَنْدَلُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، فَمَا خَوْفُهُمْ؟ قَالَ: «يَا جَنْدَلُ، فِي زَمَنِ كُلِّ وَاحِدٍ مِنْهُمْ سُلْطَانٌ يَعْتَرِيهِ وَ يُؤْذِيهِ، فَإِذَا عَجَّلَ اللَّهُ خُرُوجَ قَائِمِنَا، يَمْلَأُ الْأَرْضَ قِسْطاً وَ عَدْلًا، كَمَا مُلِئَتْ جَوْراً وَ ظُلْماً- ثُمَّ قَالَ (عَلَيْهِ السَّلَامُ)- طُوبَى لِلصَّابِرِينَ فِي غَيْبَتِهِ، طُوبَى لِلْمُقِيمِينَ عَلَى مَحَجَّتِهِمْ، أُولَئِكَ وَصَفَهُمُ اللَّهُ فِي كِتَابِهِ، فَقَالَ: الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ «١»، وَ قَالَ: أُولئِكَ حِزْبُ اللَّهِ أَلا إِنَّ حِزْبَ اللَّهِ هُمُ الْمُفْلِحُونَ «٢».
Yace : " Yaa Ma'aikin Allah, menene sunansa ?" Yace :
" BA A AMBACE SHI BA SAI YA BAYYANA. "
Sai Jandalu yace : " Yaa Ma'aikin Allah, haqiqa mun sami ambatonsu cikin Attaura, kuma haqiqa Musa Bn Imrana (A. S) yayi mana bushara dakai, da kuma wasiyyanka daga cikin zuciyarka. "
Sa'an nan Manzon Allah (S. A. W. W) ya karanta :
" ALLAH YAYI ALQAWARI GA WADANDA SU KAYI IMANI DAGA CIKINKU KUMA SUKA AIKATA KYAKKYAWA (cewa) ZAI HALIFANTAR (shugabantar) DASU CIKIN QASA KAMAR YADDA YA HALIFANTAR DA WADANDA KE GABANINSU, KUMA ZAI TABBATAR MUSU DA ADDININSU WANDA YA YARDAR MUSU, KUMA ZAI CANZA MUSU DA AMINCI BAYAN TSORO. "
Sai Jandalu yace : " Yaa Ma'aikin Allah, menene tsoron nasu ?" Yace :
" YAA JANDALU ! CIKIN ZAMANIN KOWANNE DAGA CIKINSU ZA A SAMI MAI IKO WANDA ZAI BIJIRO MASA KUMA YA CUTAR DASHI. IDAN ALLAH YA GAGGAUTA FITOWAR JAGORANMU ZAI CIKA QASA DA DAIDAITO DA KUMA ADALCI, KAMAR YADDA MUGUNTA DA ZALUNCI YA CIKATA. "
Sa'an nan (A. S) yace :
" DADIN YA TABBATA GA WADANDA SU KAYI HAQURI YAYIN GHAIBARSA (fakuwarsa), DADI YA TABBATA GA WADANDA SU KAYI TSAYIN DAKA AKAN MASU JAYAYYA DASU, WADANAN SUNE WADANDA ALLAH YA SIFFANTA SU CIKIN LITTAFINSA, YACE :
" SUNE WADANDA SU KAYI IMANI DA GHAIBU. "
Kuma Yace : " WADANNAN SUNE RUNDUNAR ALLAH. KU SAURARA ! LALLE RUNDUNAR ALLAH ITA CE MAI RABAUTA. "
قَالَ ابْنُ الْأَسْقَعِ: ثُمَّ عَاشَ جَنْدَلٌ إِلَى أَيَّامِ الْحُسَيْنِ بْنِ عَلِيٍّ (عَلَيْهِ السَّلَامُ)، ثُمَّ خَرَجَ إِلَى الطَّائِفِ، فَحَدَّثَنِي نُعَيْمُ بْنُ أَبِي قَيْسٍ «٣»، قَالَ: دَخَلْتُ عَلَيْهِ بِالطَّائِفِ وَ هُوَ عَلِيلٌ، ثُمَّ إِنَّهُ دَعَى بِشَرْبَةٍ مِنْ لَبَنٍ فَشَرِبَهُ، وَ قَالَ: هَكَذَا عَهِدَ إِلَيَّ رَسُولُ اللَّهِ (صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَ آلِهِ)، أَنْ يَكُونَ آخِرُ زَادِي مِنَ الدُّنْيَا شَرْبَةً مِنْ لَبَنٍ، ثُمَّ مَاتَ (رَحِمَهُ اللَّهُ)، وَ دُفِنَ بِالطَّائِفِ، بِالْمَوْضِعِ الْمَعْرُوفِ بِالْكَوْرَاءِ."
Ibn Asqa'i yace : " Sa'an nan Jandalu ya rayu zuwa kwanukan Hussaini Bn Aliyu (A. S). Sa'an nan ya fita zuwa 'Da'ifa.
Nu'aim Bn Abiy Qais ya bani labari yace : " Na shiga zuwa gare shi a 'Da'ifa alhali ba shi da lafiya, sa'an nan yayi kira a kawo masa abin sha na daga Nono, ya sha shi. Kuma yace :
" KAMAR HAKA MANZON ALLAH (S. A. W. W) YAYI MIN ALQAWARI CEWA SHI ZAI KASANCE QARSHEN GUZURINA DAGA DUNIYA SHA NE DAGA NONO. "
Sa'an nan ya rasu (R. L), kuma aka binne shi a 'Da'ifa a gurin da aka fi sani da KUURAA'A. "
١) البقرة ٢: ٣.
(٢) المجادلة ٥٨: ٢٢.
(٣) في المصدر: نعيم أبي قبيس.
البرهان في تفسير القر
(٦)- تأويل الآيات ١: ٣٦٨/ ٢٢١.
(٧)- كفاية الأثر: ٥٦.
(١) في المصدر: قد هتك.
(٢٢) في «ج، ي، ط»: واثلة بن الأصقع بن قرضاب، و في المصدر: واثلة بن الأشفع، راجع تهذيب التهذيب ١١: ١٠١.
البرهان في تفسير القرآن، ج٤، ص: ٩١
YAA ALLAH KA TABBATAR DAMU KAN WILAYA GA DUKKAN LIMAMAN SHIRIYA GOMA SHA BA (12)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.
(08137925034)
2nd December, 2023/ 19th Jimada-Ulah, 1445.
Tags:
Daga marubuta