Daga - Mahadi Tukur Almizan.
Da misalin ƙarfe 11 na safiyar yau Alhamis wanda yayi dai dai da 16 ga watan Nuwamba / 2 ga watan Rabi'us-Sani, ƴan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) sun fito muzaharar nuna goyon baya ga al'ummar Falasɗinu a Birnin Kaduna.
An fito wannan muzahara ne domin jaddada rashin amincewa tare da alhinin ta'addancin da Isra'ila ke yi akan al'ummar Palasɗinu wanda ya haɗa har da mata da ƙananan yara.
Almajiran na Sheikh Zakzaky (H) sun fito maza da mata har ma da ƙananan yara, anfaro muzaharar daga NEPA Roundabout dake tsakiyar birnin Kaduna, muzaharar na tafiya har zuwa gaban Ofishin Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam (Human Right Commission Office), anan ne jami'an tsaron ƴan sanda bangaren Mopol suka afkama Muzaharar.
Jami'an Mopol ɗin sun buɗe wuta da harsashi mai rai akan masu zanga zangar tare da harba barkonon tsohuwa.
Buɗe wutar da jami'an tsaron suka yi yayi sanadiyyar rasa rayukan mutum 2.
Waɗanda suka rasa rayukan nasu sune Shaheed Sidi Anas mai kimanin shekaru 30 a duniya da kuma wani yaro Shaheed Muhsin Abubakar mai kimanin shekaru 15 da haihuwa.
Wannan shine Dan Okada da jami'an tsaro suka harbe lokacin da suka bude ma almajiran na Sheikh Zakzaky (H) wuta.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update