YADDA PROGRAM DIN MAULUDIN MANZON ALLAH(S) YA GUDANA A GARIN PORTHAR COURT RIVERS STATE
@Ma'asuma Nigerian News Updates
Real Naseer Umar Alhassan ✍️
Insha Allah Bayan bude taro da Addu'a tare da karatuttukan AlQu'ani mai girma daga bakin dalibai da kuma manyan mutane. Wanda daga nan sai aka gabatar da ziyarar fiyayyan Halitta Annabi Muhammad (Saww) bayan kammala ziyarar sai aka bawa shu'ara fili domin gwangwaje wurin da gwalagwalan baituka yabon Manzon Allah (Saww) tare da alayan sa .
Bayan suma sun kammala sai aka gabatar da sarkin malaman Addinin Musulunci na garin Phortha Court baki daya Wato Malam Halliru Imam Alhamdulillah shima Malam ya dan tofa albarkacin bakin sa inda ya fara dacewa da yaso yabar wajan taron Mauludin nan da misalin karfe 10:00pm amma saboda shaukin Mauludin da kuma yadda wurin ya kasance gashi yanzu yakai har kafer 11:00pm saura sannan ya kara da cewa ko iya haka aka tsaya anyi Mauludi saka makon dan baitocin da aka gabatar.
Daga nan sai aka gabatar da Babban bako mai jawabi wato Ashsheik Ishaq Misau wanda shine zaya gabatar da jawabin awurin Na'am shehin Malamin yayi ɗauko tinda farko rayuwar Ma'aiki (Saww) tare da fadin wasu darussan Daya kamata muyi koyi dasu kamar irin su
Kyakykyawar Mu'amala
Rikon Amana
Fadar Gaskiya
Rikon Addini
Da Kuma taimako
Da sauran su dan suna da yawa bayan ya kammala shima sai aka raba kayan walima aka sallami kowa
Ilahee ya kara hada kawukan Musulmi tare da taimakon musulunci da Musulmai bihakki Muhammad Wa'aalih 🤲🙏
Hoto: Na Shaheeda Bawan Allah
14/5/1445. 26/11/2023