Daga - Mahadi Tukur Almizan
Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta kama wata mata da da tayi ƙoƙarin siyar da wata ƙaramar yarinya ƴar kimanin shekaru uku.
Matar mai suna Blessing Jeremiah ta sace yarinyar ne kuma tayi ƙoƙarin tura ta zuwa ga wanda ya siya yarinyar akan kuɗi Naira dubu ɗari biyar da talatin (530,000).
Matar ta saci yarinyar ne a unguwar Tudun Natsira da ke garin Minna babban birnin jihar Neja, an kama ta ne yayin da take ƙoƙarin hawa babbar motar sufuri domin kai yarinyar garin Nnewi da ke jihar Anambra can kudancin Najeriya.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Abiodun Wasi'u ya tabbatar da faruwar lamarin a juya juma'a kuma ya bayyana cewa an miƙa yarinyar da mahaifiyar ta.
Jami'in ya bayyana cewa a ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata suka kama matar mai suna Blessing Jeremiah mai kimanin shekaru 51 wadda ke zaune a Ƙetaren Gwari a cikin garin Minna a lokacin da take ƙoƙarin hawa motar sufuri a Maitumbi byepass.
Bayan kama matar ta bayyana cewa tayi niyyar kai wannan yarinya ne garin Nnewi dake jihar Anambra a can kudancin Najeriya, wani mutumin ne ya bata kwangilar samo ɗiya mace akan kuɗi Naira 530,000, a yayin da aka kama matar an samu zunzurutun kuɗi har Naira 230,000 kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.
✍️ Mahadi Tukur Almizan