Daga - Mahadi Tukur Almizan.
Wani mai gyaran wutar lantarki ya gamu da ajalin sa a lokacin da ya hau Pole domin gyara wutar makotansa.
Lamarin ya faru ne da mutumin mai suna Dare a Unity Estate Aregbe dake Obantoko a Abeokuta Jihar Ogun.
Lamarin ya faru ne a jiya Talata inda ya hau Pole domin taimakawa ya gyara wutar makocinsa mai suna Elijah.
An samu katsewar wuta ne daga wayoyin dake jikin Pole ɗin ta makocinsa.
Mai magana da yawun command ɗin ƴan sandan jihar ta Ogun Omolola Odutola ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
Omolola ta bayyana cewa an nemi marigayin ya taimaka ya canza wayar da ke da matsala a Pole ɗin.
Ta ƙara da cewa hukumar ƴan sandan jihar zata gudanar da bincike akan faruwar wannan lamari, za su yi ƙoƙarin gano cewa ko wannan gyara da aka nemi marigayin yayi, aiki da iya waɗanda ke da horo daga ma'aikatan kamfanin raba wutar lantarki na jihar (IBEDC) kaɗai ke iyayi.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update