Shugaban Ƙasar Venezuela Nicolas Maduro Yayi Kira Ga Al'ummar Duniya Akan Al'amarin Palasɗinawa.

 


Daga - Mahadi Tukur Almizan

Shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro ya yi kira ga magoya bayan Palasɗinawa cewa su cigaba da fitowa kan tituna har sai an dakatar da Isra'ila daga kai hare hare Gaza.


Ya nemi al'ummar duniya su shiga sahun masu taimakawa Palasɗinawa wajen ƙwatar ƴancin su na rayukan su da kuma ƙasar su, ya kuma nemi a cigaba da kiraye kirayen kawo ƙarshen ta'addancin Isra'ila a Gaza.


Maduro yayi waɗannan bayanai ne a lokacin da yake gabatar da jawabin ƙarshen mako ta talabijin a ranar Talata, inda ya bayyana cewa " Dole ne al'ummar duniya su fito su tsaya a tituna, saboda  muyi nasara a wannan yaƙin na samar ma Palasɗinawa ƴancin rayuwa da kuma samar masu da ƙasar su mai zaman kanta".


Ko a makon da ya gabata , Maduro ya bayyana cewa dole ne ƴan adamtaka tayi aiki wajen ƙalubalantar Isra'ila akan ta'addancin da take yi a Gaza, ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin da yake karɓar baƙuncin jakadan Palasɗinu  Fadi Al-Zaben a birnin Caracas.


A lokacin ya bayyana cewa " Ana kashe mata da yara a cikin mummunan yanayi".


" Dole ne mu tashi da murya ɗaya mu kawo ƙarshen ta'addancin Isra'ila akan al'ummar Palasɗinu". Wannan wasu daga kalaman Maduro ne a ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata.


Shugaban na Venezuela dai yana ta matsala lamba akan dakatar da Isra'ila daga kai hare haren a Gaza.

Zaku iya samun datar kowane Network cikin sassauƙan farashi a FADAKDATA 👇



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post