Lokacin da ciki ya shiga jikin mace akwai wasu sinadarai da suke canza yanayin jiki tun daga shigar ciki har zuwa haihuwa ana Kiran su Hormones
Wannan hormones sune kamar haka:
1. Estrogen
2. Progesterone
3.Relaxin
4. Oxytocin
5. Human chorionic gonadotropin
6. Human placental Lactogen
7. Prolactin
Wadannan hormones sune suke canza yanayin jiki su saka Masa laulayi kamar haka:
1. Amai
2. Tashin zuciya
3. Ciwon ciki
4. Yawan gajiya
5. Fitar ruwa daga gabansu
6. Ciwon kafa da kumburin kafa
A wasu lokuta akan samu wasu mata basayin Laulayi musamman matan da suka yi cikin shege.
BABBAN DALILIN DAKE HANA LAULAYI
Kasantuwar Al'adun Kasar Hausa cikin shege wani babban al'amari ne mata suna fuskantar tsangwama daga Gurin al'umma suna kamuwa da wata larura ta damuwa wato 'EMOTIONAL STRESS'
Hakanan ma koda matar Aure ce idan tana fama da Emotional Stress to ya na iya hana ta yin Laulayi.
EMOTIONAL STRESS Yana sakawa a samar da wasu sinadaran kamar haka:
1.cortisol
2. Corticotropin Releasing Hormones
Wadannan sinadarai suna dakatar da aikin wasu daga sinadaran da suke saka laulayi Amma Kuma suna cutar da yaron da uwa take dauke dashi.
SAKAMAKON HAKA MATA MASU CIKIN SHEGE BASAYIN LAULAYI AMMA KUMA AKAN HAIFI YARO BABU RAI KO KUMA DA RASHIN LAFIYA.