Daga Mahadi Tukur Almizan.
Kamar yadda muka sani cewa a cikin shekarar da ta gabata wato 2022 babban bankin Najeriya ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira 1000,500 da 200, wanda aka sanya ranar da za a daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin kafin daga baya aka ɗaga.
Sai dai a jiya Talata Babban Bankin Najeriya ya bayyana aniyar ƙara tsawaita lokacin daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, bankin ya bayyana cewa za a cigaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin, babu ranar da za a daina.
CBN ya bayyana cewa dukkanin reshen shi dake faɗin ƙasar nan zai cigaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin.
" Al'umma su cigaba da more tsofaffin takardun kuɗin a dukkanin harƙallolin su na yau da kullum kasuwanci da na ma kashewar ɗai-ɗai" a cewar babban bankin na Najeriya.