RAYUWAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H);TAFIYE-TAFIYENSA DA KUMA ALAQARSA DA AL’UMMAH

 


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe masu yawa a sassa da dama na duniya, kusan ma ba wani sashe na duniya da bai je ba, kama daga Asiya, Turai, da ƙasahen Afirka. Misali, a yankin Asiya ya je ƙasashe kamar su; Iran, Iraqi, Saudi Arabiyya, Dubai, Lebanon, Malesiya da sauransu. A ƙasashen Afirka kuwa ya je Sudan, Ghana, Saliyo, Mali, Habasha, Nijar, Kenya, Afirka ta Kudu, Libiya da sauransu. Sannan ya je manyan ƙasashen duniya masu tinƙaho irinsu Birtaniya, Amurka, Rasha, Faransa da sauransu. Dukkanin waɗannan tafiye-tafiye ya yi su ne ta hanyar gayyata bisa dalilai na addini, ko halartar tarurrukan ƙarawa juna ilimi.


“Haka nan in muka dawo nan cikin gida za mu ga cewa Sayyid Zakzaky (H) ya je birane da ƙauyuka masu yawa a cikin ƙasar nan don isar da wannan Da’awa da yake yi, kai mutum ma zai iya dukan ƙirji ya ce a jihohin ƙasar nan musamman ma na arewawacin ƙasar, to, ba jihar da bai je domin isar da wannan saƙo na Allah Ta’ala ba” (Tarihin Harkar Musulunci, shafi na 23).

MUSULMI : Abu ne sananne ga kowa cewa Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya fi kowane malami a Nijeriya kyakkyawar alaƙa da sauran musulmin da ba fahimtarsu ɗaya ba, domin ko kaɗan ba ya ƙyamar musulmi na kowace Mazhaba ko Aƙida, hasali ma ya fi kowa jin zafi bisa rashin jituwar da ke tsakanin ƙungiyoyin musulmi. Kullum a cikin sa’ayi na haɗa kan musulmi yake, damuwarsa ita ce, aƙalla musulmi su yarda su dena aibata juna da sukan juna da kafirta junansu. Daga cikin ƙoƙarin Shaikh Zakzaky (H) na haɗa kan musulmi ya sunnantawa kansa da almajiransa ziyarar Malamai na ƙungiyoyin musulmi daban-daban, daga loƙaci zuwa loƙaci Shaikh (H) yakan tashi takanas ya je gidajen manyan malamai ya ziyarce su don neman kusanci da fahimtar juna.


Sannan duk garin da ya je don wa’azi ko halartar wani taro, yakan je ziyara ta sada zumunci da neman kusanci da fahimtar juna ga manyan malamai na garin, yakan ziyarci malamai ne mabanbanta na ƙungiyoyin musulmi. Sannan ya hana almajiransa warewa ko gina masallatansu na ƙashin kansu, don hakan zai ƙara kawo rarraba da farraƙa ne a tsakanin musulmi, wannan ya sa duk inda almajiran Shaikh Zakzaky (H) suke, suna Sallah ne a masallatai na al’ummar musulmi, kuma a bayan limamai na waɗannan sassan musulmin, tattare da cewa suna riƙo ne da tafarkin Ahlul-Bait (AS) wato Ja’afariyyah.

KIRISTOCI: Ko ba a faɗa ba duniya shaida ce game da kyakkyawar alaƙar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da Kiristoci da ma sauran mabiya addinai a Nijeriya, domin in banda Shaikh (H) ba wani malami da Kiristocin Nijeriya ke yabawa salon Da’awarsa kamarsa. Ƙungiyoyin Kiristoci daban-daban sun sha rubutawa Shaikh Zakzaky (H) takardar yabo da godiya bisa gudunmawar da almajiransa suka ba su, na tseratar da rayukansu, ko na kariya ga dukiyoyinsu ko ga wuraren kasuwancinsu a lokutan rigingimun addini ko na ƙabilanci ko na siyasa.


A wurin Shaikh Zakzaky (H) hanya mafi dacewa ta yin jihadi ga Kiristoci ita ce hanyar isar musu da saƙon musulunci na haƙiƙa ta kyakkyawar hanyar da za su fahimta su gamsu, ba wai ta hanyar hantara ko far musu da kisa ko ƙona dukiyoyi da wuraren ibadarsu dan kawai sun zaɓi su zama kiristoci ba.


__Faruq Sani Kudan

Zakzaky ikon Allah

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post