MUZAHARAR NUNA GOYON BAYA GA PALESTINE A BABBAN MASALLACIN JUMMA'A NA KASA DAKE ABUJA DUK DA BARAZANAR JAMI'AN TSARO

 


Harkan Musulunci Karkashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ta gudanar da Muzaharar nuna goyon bayanta ga al'ummar Falasdinu da kasar Isra'ila ke zalunta.



Muzaharar an gudanar da ita ne bayan Idar da Sallar Jumma'a a harabar Babban Masallacin kasa na Abuja, inda Daruruwar al'umma Maza da mata da yara suka fito, dauke da Tutar Palestine tare da hotuna na nuna goyon baya gasu al'ummar ta palestine. 



Inda Muzaharar ta fito har wajen masallacin, aka tafi da ita inda aka saba kulle Muzahara, a lokaci guda Jami'an tsaro suna kokari hana Muzahara ci gaba da gudana, amma cikin ikon Allah an kai ta wajen da aka saba har aka kona haramtacciyar Tutar Isr*il*, sannan aka rufe. Ana rufe Muzaharar sannan jami'an tsaro suka fara harba Borkono tsohuwa kan masu Mazaharar, zuwa hada wannan rahoton bamu samu tabbacin wadanda aka harba ko aka Kama ba, ammah dae ansha barkonon tsohuwa.





AliAssajjad Ibn Taheer 

Isa Charis

24th November, 2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post