MU'UTAMAR ƊIN ISMA NA ƘASA ƘARO NA 27 A GARIN BAUCHI

 



Illolin Zubar da Shara ba Bisa Ƙa'ida ba: Barazana ga Rayuwar Al'umma na daga cikin jawaban da aka gabatar a wajen taron wanda Malami daga Hukumar kula gami da tsaftar muhalli na jihar Bauchi, Dr. Ibrahim Kabir ya gabatar.


Cikin jawabin Dr. Kabir ya ja hankalin mahalartan akan muhimmancin tsaftace muhalli tare da illolin da ke tattare da zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba wanda yin hakan ke da illa ga rayuwarmu na yau da kullum.



Daga cikin hanyoyin zubar da shara akwai, ƙonawa, niƙewa, rufewa a rami guda, waɗannan da ma wasu suna daga cikin hanyoyin da Dr. ya bayyana a matsayin hanyar da ya kamata al'umma su bi wajen sarrafa sharan da ya taru a muhallinsu.



Matakan da aka fadi na lalacewar muhallqo sakamako gurbɓta da take yi da shara, yana da alaka ne da yawan al'umma, da kuma rashin ɗa'a na mutane a yau na zubar da shara a guraren da bai dace ba.


SHAWARWARI

Gwamnati ta samar da muhallan zubar da shara gami da samar da dokar hukumta duk wani wanda ya zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba.

Gwamnati ta dawo da tsarin gabatar da sharan bai ɗaya na wata-wata ga al'ummar da take mulka domin samar da muhalli mai inganci.


©Bauchi Media Forum

25-11-2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post