Harkar Musulunci Karkashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), ta fara gudanar da taron mu'utamar amm Wanda ke gudana garin lafia dake Jahar Nasarawa.
Da yammacin yau Jumma'a 17/ November Shekarar 2023, an fara taron da budewa da addu'a Wanda Malam Muhammad Ghali ya gabatar, sannan Malam Muhammad Aliyu ya gabatar da Karatun Alkur'ani Mai girma. Daga bisani mawaka suka gudanar da majalisin wakokin Harka, sannan Ammah Suwaiba Bauchi ta gabatar da Jawabin maraba da Baki, sai aka gabatar da mai Jawabi Sheikh Muhammad Bature Sokoto, Wanda yayi Jawabi maudu'i mai taken (kalman Shahada).
Daga karshe an bawa Malam Salihu Baba ya rufe wannan taron da addu'a.
Wannan shine Kashi na farko kenan a yau.
#MuutamarLafia2023
#LafiaConference2023
17/November2023