Daga - Mahadi Tukur Almizan
Wani jirgin ruwa ɗauke da manoma a gundumar Ubbe dake jihar Nasarawa ya yi hatsari a yayin da yake tsallaka rafin ƙauyen Hunki dake ƙaramar hukumar Awe ta jihar Nasarawa.
Manoman dai sun gamu da wannan hatsari ne akan hanyar su ta dawowa daga gonar shinkafa.
Hatsarin ya afku ne a daren jiya Litinin, waɗanda hatsarin ya rutsa da su sune, Aiko Misra, Mashack Dauda, Shedrack Dauda da wani mai suna Alkali Congo.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar DSP Ramhan Mandela ya tabbatar wa jaridar DailyPost faruwar wannan lamari.
Sai dai DSP Ramhan ya bayyana cewa har yanzu ba a gano gawar matuƙin jirgin ba, amma dai an ceto gawarwakin sauran mutane huɗu da sukayi hatsarin.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update