Mutane da yawa Suna ma "Shi'a kallon wani Abu daban Kuma, suna Mata mummunan zargi, da Ance wane Dan shi'a ne Shikenan Kamar Ance wane kafiri ne wa'iya zibillah🤦🏻♀️🥹.
Kalmar "shi'a" Dai kalmar Larabci ne Wanda take Nufin "Mabiya" ko "Jama'a" A fassara mafi Inganci. A Addinince Yana Nufin "Magoya Bayan Imam Ali (A.S)"
SU WANE NE YAN SHI'A?
1__ 'Yan "shi'a" Sune wadanda suka miqa Wilayan su ga Imam Ali (A.S) Sukayi Imani Dashi a Matsayin Wasiyyin Annabi (S) majibincin Lamarin su, Kuma Imami na farko.
2__'Yan shi'a sune wadanda suka yi Ruqo da wasiyan manzon Allah (S) Suka Riqe Al'qurani da Ahlulbaity (A.S)
3__ 'yan shi'a sune Sukayi Imani da Imamai Goma shabiyu 12 A bayan Manzon Allah (S)
4__An Tambayi Manzon Allah (S) su waneye kairul Bariyya? Sai yace " 'HUM ALIYU WA SHI'ATIHI
(sune Aliyu da Jama'arsa)".
Mu Hadu a Kashi na Gaba insha Allah inda zamuji matsayin Imam
Ali (A.S) a Addini, matsayin shi a wajen Annabi (S), da karamomin shi.
__Khauthar Muhammad Auwal Aqeelah
✍🏻🌹✍🏻