Daga - Mahadi Tukur Almizan
Fadar White House na cigaba da tura ƙarin makamai zuwa Isra'ila duk da cewa Isra'ila na amfani da waɗannan makamai wajen kashe al'ummar Gaza.
Ɗaruruwan masu zanga zangar goyon bayan Palasɗinawa ne suka shiga tashar jiragen ruwa ta "Tacoma" dake birnin Washington a yau Talata 7 ga watan Nuwamba,' domin hana jirgin dakon makamai da kayan soji zuwa Isra'ila motsawa daga tashar kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
Masu zanga zangar sun nuna takaicin su na baiwa Isra'ila waɗannan makamai da suke amfani dashi wajen kashe al'ummar Gaza, wanda zuwa yanzu sun kashe Palasɗinawa sama da dubu 10, mafi yawa daga ciki mata ne da yara a cikin wata ɗaya.
Ɗaya daga cikin masu zanga zangar Wassim Hage daga "Arab Resource and Organization Center (AROC) ya bayyana cewa " Muna buƙatar a tsagaita wuta yanzu. Muna buƙatar a daina kashe al'ummar Gaza yanzu. Muna buƙatar ayi nazari tare da ɗaukar mataki dangane siyasar Amurka kan ƙasashen waje da taimakon da Amurka ke baiwa Isra'ila".
Ya ƙara da cewa an tabbatar ma (AROC) cewa an shirya jirgin ruwa ɗauke da makamai zai bar wannan tashar zuwa Isra'ila, taimako domin cigaba da kashe al'ummar Gaza.
Sai dai kafar yaɗa labarai ta Aljazeera da ta ruwaito labarin bata tabbatar cewa wannan jirgin ruwa na ɗauke da makamai ba ko akasin hakan.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update