Daga - Mahadi Tukur Almizan
A daren ranar juma'ar da ta gabata masu garkuwa da mutane sun afka Garin Kiyawa kuma sunyi nasarar shiga gidan shugaban ƙaramar hukumar ta Kiyawa har sun kwashe matan sa biyu.
Wata majiya ta tabbatar ma jaridar Daily post maharan sun yi harbe harbe a sama lokacin da suka shiga garin wanda hakan ya firgita al'ummar garin.
Ɗaya daga cikin matan shugaban ƙaramar hukumar da aka ɗauka tana ɗauke da tsohon ciki, wanda zata iya haihuwa a kowane lokaci.
SP Lawal Shisu mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ta Jigawa ya tabbatar ma manema labarai faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa hukumar ƴan sanda tana nan tana ƙoƙari domin ganin an ƴanto matan da aka kama.
Zuwa yanzu dai masu garkuwa da mutanen basu tuntuɓi iyalan waɗanda suka kama ba.
✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update.