KAƊAN DAGA CIKIN JAWABIN SYED NASRALLAH DA YA GABATAR AKAN FALASƊINAWA
Ma'asumah Nigeria News Update
Cikin Jawabin Syed Nasrallah: Muna yiwa dukkan shahidan da suka rasa rayukansua yaƙin da suke yi da ƙ*sar Is*ra*l jinjina, Mu sani yaƙi da Is*ra*l Misali ne bayyananne na tafarkin Allah.
Babu wata magana da za ta iya bayyana juriya da dagewar mutanen Gaza Har zuwa yankin yammacin Kogin Jordan. Duniya gaba ɗaya tasan irin Wahalhalun da al'ummar Falasɗinawa suke ciki a cikin Shekaru 7t da suka Gabata.
Muna Allah wadai da yadda ƙasashen duniya suka yi watsi da laifukan da Is*ra*l ke yiwa Falasɗinawa. Yanƙurin da muka aka sa masa suna Ambaliyar ruwa Al-aqsa, ta tabbatar da gwagwarmayar Falasɗinawa mai cin gashin kanta daga al'amuran yankin. Wannan yunkurin na Ambaliyar ruwa ta Al-aqsa ta tabbatar da cewa Is*ra*l tafi gidan gizo-gizo rauni.
Sadaukarwar Falasɗinawa za ta yi Tasiri sosai ga makomar yankin baki ɗaya, Sabbi shaidu sun nuna cewa Sojojin Is*ra*l ne suka kashe fararen hular rana 7 ga Oktoba, ba Hamas ba.
Aikata kisan "kiyashin ga Fararen Hula" shi ne kawai abin da sojojin Is*ra*l suka kware a kai. Wannan rikicin ba zai ƙare ba sai da nasarar tsayin daka daga dakarun Musulunci. Waɗanda suka yi shiru kan abubuwan da Isr*'*l ke aikatawa a Gaza dole ne su sake Tunani akan Mutumtaka.
Burinmu na farko shi ne kawo karshen yaƙi a Gaza za ta kasance moriyar ƙasar da ƙasashen makwabta, Is**l sun mai da gwamnatocin Larabawa lusarai ababen wasan su. Saboda sun kasa tallafar mutanen Gaza da suka jikkata.
Ma'asumah Nigeria News Update