JINKIRIN AIWATAR DA ADALCI SHI MA RASHIN ADALCI NE.!



Tana ta ƙara tabbata cewa Alƙali Sulaiman Belgore azzalumi ne, kuma shi ya fi kowa zaƙewa a wajen cuta ma ƴan uwan mu da ake tsare da su a Abuja.

Sati ɗaya ya rage a koma kotu don ci gaba da shari'ar da Alƙali Sulaiman Belgore yake yi tsakanin ƴan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (H) da Kwamishinan ƴan sanda a Abuja, kamar yadda shi da kan shi ya sanya ranakun 29 da kuma 30 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki bayan shafe sama da watanni 8 kotun tashi bata zauna ba. Kamar yadda ya saba a take-taken sa na ganin ya ci gaba da tsare ƴan uwan mu, yau ma Alƙali Belgore ya aiko da cewa kotunsa ba za ta zauna a ranar Laraba 29 ga wata ba, ba kuma tare da bayyana dalilin hakan ba.

A bayyane yake zahiri cewa zuwa yanzu Alƙali Sulaiman Belgore shi yake da muradin ci gaba da tsare waɗannan raunana da basu aikata laifin komai ba, kamar yadda ya ambata tun a ranar 30 ga watan Nuwambar shekarar 2021 lokacin da yake gabatar da hukuncin sa a kan takardar "NO CASE SUBMISSION" da lauyan ƴan uwan ya gabatar a gaban kotu, yau kimanin shekara biyu, inda ya bayyana cewa "ba zai saki ƴan uwan ba, yana da bukatar su tsaya su kare kawukan su da kan su, tare da amsa masa wasu tambayoyi".

Muna kira ga dukkan masu Imani da zuciya ta ƴan adamtaka da su taya mu yayata zaluncin da wannan Azzalamin yake yi a kan ƴan uwan mu da sunan Shari'a, ta hanyar tsare sama da mutum 50 da 80% nasu yara ne da aka kama su suna ƴan ƙasa da shekaru 18, tare da yin Allah wadai da baƙin zaluncinsa.

Allah ya kunyatar da shi, da duk masu taimaka masa ko jin daɗin aikin sa. Allah ya ƙara ma waɗannan bayi nasa haƙuri da jure ma jarabawoyi, sannan Allah ya gaggauta basu mafita.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post