Da suke bikin maulidin Sayyida Zainab (SA) a zone ɗin Uwaisul Qarni (Gombe), matasan Zainabawan Jaish Shaheed Ahmad Zakzaky sun ziyarci gidan Marayu da Asibiti yau Alhamis.
Ziyarar tasu a safiyar yau Alhamis sun fara da Asibitin Pantami ne, wanda isar su keda wuya suka sami tarba daga ma'aikatan Asibitin, sannan suka isa dasu dakunan marassa lafiya bayan sun gabatar da makasudin zuwansu.
Zainabawan sun gabatar da kyautuka ga marassa lafiya, kuma alhamdulillahi ma'aikatan asibitin da marassa lafiya sunji dadi da yaba wannan ziyarar, sannan akayi hotuna suka rako yan uwan har waje akayi ban kwana.
Ziyarar daga nan ta zarce zuwa gida Marayu dake tsohon Mile Uku, daga isar tawagar sun sami kyakkyawar tarba daga babban mai kula da gidan da sauran ma'aikatan gidan, sannan suka isa da Zainabawa cikin.
Bayan gabatar da makasudin ziyarar an fito da Marayun, anan aka gaggaisa dasu tare da gabatar da kyautuka da ake tafe musu dashi, yara sunji dadi sosai da wannan ziyarar, sannan akayi hotuna tare dasu da mai kula da gidan.
Sunyi godiya da ziyarar da kuma yiwa Jagora (H) addu'a da fatan nasara, tare da kuma fadin a koda yaushe yan uwa suka shirya irin wannan ziyara suna maraba da ita adukkan wuraren da aka ziyarta. Ga wasu daga cikin hotunan ziyarar.
-JASAZ UQM
23-11-2023