Daga - Fatima Adamu Tinja..✍️
Imani Wata hanya ce da ke nuni da gasgatawa da sallamawa hade da aikatawa da bin umarni da amince wa mahalicci. Mutum kan yi Imani da Allah saboda gasgatawa da ya yi cewa Shi ne Ya halicce shi, Ya kuma tsara komai nasa. Abu ne mai Wahala mutum ya gasgata da abin da zuciyarsa ba ta amince da shi ba. Duk wani mai takama da koyi da Addini idan har ya zama bai ba da gaskiya da abin da Addini ya umarce shi ko ya hane shi ba, to lallai ya zama marar imani na hakika.
Kowane ɗan adam Yana da linzami da iyaka da Allah Mahalicci Ya yi masa, idan har ka zama mai kiyaye iyakokin da Allah Ya yi maka da kyautata ayyukan da ya umarce ka ka yi, to sai ka ji koda Yaushe ranka ya yi dadi, domin shi imani hanya ce ta warkar da gabbai daga dukkan wani abin ki. Idan mun yi duba ya zuwa ga wadanda suka ba da gaskiya, suka zama suna aiki da shi, to za ka iske su masu tsananin koshin lafiya da zaman lafiya.
Na sha ji masu bada magungunan gargajiya da likitoci suna fadin cewa, "Mu ba da magani shine aikinmu, amma waraka tana hannun Allah." Kuma mafi yawan su sun yi imani da cewa, ba dabararsu ce ke warkar da mutane ba, Allah ne ke warkar da marar lafiya. Wani babban likita ya fada cewa, "Idan har Ma'aikatan lafiya zasu ji aransu lallai Allah Shi ne ke warkarwa, Mu kawai neman taimakonsa muke yi, to lallai da asibitocimmu sun zama wuraren samun lafiya".
Sau tari mukan tsinci kammu cikin halin ƙa-ƙa-nikayi, Rayuwa ta zama ba gaba-ba-baya. Sai ka ga mun dauki damuwa mun tayar da hankalinmu, har hakan ya sa zuciyarmu ta samu matsala, wanda kuma kan haifar da matsaloli ga sauran gabban jikinmu. Kamar hauhawar jini, shanyewar barin jiki da sauransu. Idan muka dubi marar lafiya da ke fama da cutar hauhawan jini, idan ya je ganin likita, bayan an duba shi, za a ba shi shawara ne da ya cire damuwa daga zuciyarsa. Domin mafiya yawan wadanda suke fama da irin wadannan cututtuka, suna fama da Wani tunani ne wanda ya takura tare da kuntata zuciyarsa, har kuma ya sanya zuciyar yin aikin da na na ta ba ne, Wanda kuma shi ne jigon da ke haifar da cuta ga dan'adam.
Hakika Ya ɗan uwa, Ka zama Mai amince wa Allah Mahalicci, kagaskata Shi, ka yarda Shi ne Mai komai, Mai iko a kan komai, kada ka biye wa son zuciyarka har ta yaudare ka ka ki yin imani da Allah. Na yarda Kai mutum ne Mai kokarin bin umarnin Allah, da dogaro da Shi, Mai mika al'amuranka gare Shi.
Don haka ka bi Wadannan hanyoyi za su taimaka maka;👇👇👇
1. A lokacin da ka tsinci kanka cikin rashin lafiya ko Wani kunci, Yana da kyau ka mika al'amuranka ga Allah, ka kuma yi Imani cewa Shi ne Mai mafita.
2. Kada tsoro ko fargabar wata cuta su sa ka shiga wani hali marar kyau. Idan kana Irin wadannan tunani sai abubuwa su Kara tabarbarewa a gareka.
3. Ka tuna a ko da yaushe cewa, Allah Ya tsara komai daki-daki tare kuma da ka'idojinsu. Amma a kan cututtuka da akwai abubuwa guda biyu; Na farko likita da zai ba ka magani, Na biyu Karfin imaninka game da Allah Shi ne mai warkarwa.
4. Ka yi Addu'a cikin jin dadi da rashinsa, ko cikin yalwa da kunci kamar yadda ya kamata kasan Allah lokacin yalwarka, Sai Allah ya San da Kai lokacin da ka shiga cikin tsanani ko kunci.
5. Ka zama Mai yi wa Wanda kake jinya fatan alheri, tare da yi masa Addu'a.
Mu sani Yah 'Yan'uwa, Imani da Allah Abu ne da ya kunshi abubuwa da yawa. Mu gujewa duk wani abu da zai taba imaninmu, Mu kuma kaskantar da kammu wajen neman taimakon Allah, Muna masu ba da gaskiya.
Masha Allah
ReplyDelete