HUMANE AI PIN: Wata Sabuwar Fasaha Ce Da Zata Iya Mayar Da Riƙe Waya Ƙauyanci



1. Humane AI Pin ƙaramin sunduƙi ne mai kama da agogon hannu samfurin 'Smartwatch'. An samar dashi ne a matsayin naurar komai da ruwanka wadda zata iya abokantakar ɗan Adam wajen samar masa da bayanai cikin hanzari da kuma biya masa waɗansu buƙatu na rayuwa.



2. Kamfanin 'Humane' wanda Imran Chaudri da Bethany Bengiorno suka kafa a shekarar 2019 ne ya samar da wannan gagarumar fasaha tare da haɗin guiwar kamfanonin Microsoft, da OpenAI, da Qualcomm da kuma T-Mobile.  


3. Humane AI na iya tattaro duk bayanan da ake so daga yanar gizo sannan ya tantance wanda ake da muradi tare da bayar dashi cikin mafi sauƙin harshe, a  mafi ƙanƙantar lokaci sama da yadda fasahar Chatgpt-4 zata yi.



4. Babu buƙatar danna madannin kira ga wanda ya maƙale fasahar Humane AI Pin a rigar sa idan har yana son yin magana da wani. Abinda kaɗai zai yi shine; ya danna na'urar, sannan yace mata "kira mini wane". 

   Idan kuwa saƙo zai tura, da zarar ya danna masarrafar, sai ya bayar da umarnin abinda za a aikewa wanda yake son turawa saƙon.


5. Fasahar tana da ƙarfin ikon fassara abinda taji daga mabanbantan harsuna. Don haka, anan gaba babu buƙatar kowa da kowa ya iya yaruka da yawa. Da zarar ka haɗu da wani mutum wanda baka iya gane abinda yake faɗa, sai ka danna madannin naurar ka umarce ta da fassara maka abinda ake magana akai, ai kuwa nan take zata fassara shi daki-da-daki cikin nutsuwa.


6. Fasahar na iya gane mabanbantan abubuwa. Don haka da zarar ka ga wani abu wanda baka gane masa ba, kai tsaye kana iya danna madannar na'urar tare da tambayar ba'asin wannan abu. Ita kuwa cikin ƙanƙanin lokaci zata ɗauki hoton abin, ta nazarce shi sannan ta fara kawo maka zantuka game dashi a sauƙaƙe.


7. Fasahar na da ikon taimakon mutum game da lafiyar sa. Tana iya bayar da shawarwari game da abinda ya kamata aci ko asha. Tana iya sanar da kai adadin sinadaran ƙara lafiyar da ka ciwa cikinka a rana tare da baka shawara. Tana kuma iya bin diddigin baccinka, ko hutunka, ko motsa jikin ka tare da ankarar da kai idan haɗari na shirin samuwa a gareka.


8. Wannan fasaha na iya zama ɗan aike, domin kuwa tana iya tuntuɓar farashin kayayyaki dake yanar gizo har ma tayi maka odar sa. Tana kuma iya ɗaukar hotuna da bidiyo idan aka buƙaci tayi hakan.


9. Kwanaki uku kenan da sanar da duniya zuwan wannan fasaha. Fasahar zata zo da lambar waya ta musamman. Kuɗin da za a soma dillancinta shine dalar Amurka 699 (Kimanin N699,000), sai kuma duk wata za a biya dalar Amurka 24 a matsayin kuɗin amfanuwa da tsarukan ta. A farkon shekarar 2024 ake sa ran soma siyar da ita ga jama'a.


©️Sadiq Umar Gwarzo

Zaku samu datar kowane Network cikin sassauƙan farashi a FADAKDATA



1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Masha Allah munamaraba da wannan cigaba

    ReplyDelete
Previous Post Next Post