HARAMCIN HASSADA A MUSULUNCI !!!

 


AYAR DA TA SAUKA DON HASSADAR DA AKE YIWA  AHLUL-BAIT (A. S) 

Ma'anar hassada shine burin gushewar wata ni'ima da Allah ya yiwa wani daga cikin bayinSa, ko dai ita ni'imar ta dawo kan wanda ke yi ko kuma dai ta gushe kowa ya rasa. 


Allah ya zargi mai hassada kuma Annabi (S. A. W. W) ya nuna mana illar yinta, domin takan cinye kyawawan ayyukan mutum ya wayi gari ba shi da komai daga ayyukansa na alkhairi. 


Allah mai girma da daukaka na cewa :


" أَمْ يَحْسُدُونَ النَّاسَ عَلَى مَا آَتَاهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ فَقَدْ آَتَيْنَا آَلَ إِبْرَاهِيمَ الْكِتَابَ وَالْحِكْمَةَ وَآَتَيْنَاهُمْ مُلْكًا عَظِيمًا." (54)

" SHIN,  ZA KU RIQA YIWA MUTANE HASSADA NE BISA ABINDA ALLAH YA BA SU DAGA FALALARSA ? HAQIQA MUN BAIWA IYALAN IBRAHIM LITTAFI DA KUMA HIKIMA, KUMA MUN BA SU MULKI MAI GIRMA. "

(SURATUN-NISA'I :54)

Allah (T) ya fifita iyalan Ibrahim (A. S) ta hanyar tayar da Manzanni (A. S) tare da littafai saukakku daga gare shi (S. W. A). Sannan kuma ya ba su mulki mai girma kamar yadda aka samu ga Annabi Yusuf da Sulaiman (A. S). 

WADANNE MUTANE NE AKE YI MUSU HASSADA  ?

Dangane da wannan aya an samo hadisai da suka fassara haqiqanin su waye ake yi musu hassada har aka saukar da wannan aya kamar yadda za mu gani cikin riwayoyin dake fiye  :

                       (1)


الباقر (عليه السلام)- نَحْنُ النَّاسُ الْمَحْسُودُونَ عَلَى مَا آتَانَا اللَّهُ مِنَ الْإِمَامَةِ دُونَ خَلْقِ اللَّهِ أَجْمَعِينَ."


Daga Imam Baqir (A. S) yace :

" MUNE MUTANEN DA AKE YIWA HASSADA BISA ABINDA ALLAH YA BAMU NA DAGA IMAMANCI KOMA BAYAN  (sauran) HALITTUN ALLAH BAKI 'DAYA  ."

المصدر :  الكافي، ج1، ص205/ بحارالأنوار، ج23، ص289/ تأويل الآيات الظاهرة، ص136/ بشارة المصطفي، ص193/ دعايم الإسلام، ج1، ص20 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص218

                          (2)


أمير المؤمنين (عليه السلام)- كَانَ نَبِيُّنَا (صلى الله عليه و آله) فَلَمَّا جاءَهُمْ ما عَرَفُوا كَفَرُوا بِهِ حَسَداً مِنْ عِنْدِ أَنْفُسِهِمْ أَنْ يُنَزِّلَ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ عَلي مَنْ يَشاءُ مِنْ عِبادِهِ حَسَداً مِنَ الْقَوْمِ عَلَى تَفْضِيلِ بَعْضِنَا عَلَى بَعْضٍ أَلَا وَ نَحْنُ أَهْلُ الْبَيْتِ آلُ إِبْرَاهِيمَ الْمَحْسُودُونَ حُسِدْنَا كَمَا حُسِدَ آبَاؤُنَا مِنْ قَبْلِنَا سُنَّةً وَ مَثَلًا."

Amirul-muminina Ali (A. S) yace : " Annabi (S. A.W.W) ya kasance (Allah yayi bayaninsa game da hassadar da Yahudawa su kayi masa, inda yake cewa)  :

" YAYIN DA ABINDA SUKA SANI (cikin littafansu game da siffofin Annabi) YAZO MUSU SAI SUKA KAFIRCE DASHI (saboda sunga ba daga cikinsu ya fito ba) SABODA HASSADA DAGA KAWUKANSU DOMIN ALLAH YA SAUKAR DA FALALARSA AKAN WANDA YASO DAGA BAYINSA. "


Hassada daga jama'a saboda fifita sashenmu akan sashe. To, ku saurara  ! Lalle mu Ahlul-Bait mune iyalan gidan Ibrahim wadanda ake yiwa hassada. Ana mana hassada kamar yadda aka yiwa Ubanninmu hassada kafin yanzu, sunnah ne da kuma misali. "


المصدر :  الغارات، ج1، ص115/ بحارالأنوار، ج33، ص133 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص220

                           (3)

أمير المؤمنين (عليه السلام)- احْتِجَاجُهُ (عليه السلام) عَلَى النَّاكِثِينَ فِي خُطْبَةٍ خَطَبَهَا حِينَ نَكَثُوهَا فَقَالَ: وَ قَدْ أَمَرَكُمُ اللَّهُ أَنْ تَرُدُّوا الْأَمْرَ إِلَى اللَّهِ وَ إِلَى رَسُولِهِ (صلى الله عليه و آله) وَ إِلَي أُولِي الْأَمْرِ مِنْكُمُ الْمُسْتَنْبِطِينَ لِلْعِلْمِ فَأَقْرَرْتُمْ ثُمَّ جَحَدْتُمْ وَ قَدْ قَالَ اللَّهُ لَكُمْ أَوْفُوا بِعَهْدِي أُوفِ بِعَهْدِكُمْ وَ إِيَّايَ فَارْهَبُونِ إِنَّ أَهْلَ الْكِتَابِ وَ الْحِكْمَةِ وَ الْإِيمَانِ وَ آلَ إِبْرَاهِيمَ (عليه السلام) بَيَّنَهُ اللَّهُ لَهُمْ فَحَسَدُوهُ وَ أَنْزَلَ اللَّهُ جَلَّ ذِكْرُهُ أَمْ يَحْسُدُونَ النَّاسَ عَلي ما آتاهُمُ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ فَقَدْ آتَيْنا آلَ إِبْراهِيمَ الْكِتابَ وَ الْحِكْمَةَ وَ آتَيْناهُمْ مُلْكاً عَظِيماً فَمِنْهُمْ مَنْ آمَنَ بِهِ وَ مِنْهُمْ مَنْ صَدَّ عَنْهُ وَ كَفي بِجَهَنَّمَ سَعِيراً فَنَحْنُ آلُ إِبْرَاهِيمَ (عليه السلام) فَقَدْ حُسِدْنَا كَمَا حُسِدَ آبَاؤُنَا وَ أَوَّلُ مَنْ حُسِدَ آدَمُ (عليه السلام) الَّذِي خَلَقَهُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ بِيَدِهِ وَ نَفَخَ فِيهِ مِنْ رُوحِهِ وَ أَسْجَدَ لَهُ مَلَائِكَتَهُ وَ عَلَّمَهُ الْأَسْمَاءَ وَ اصْطَفَاهُ عَلَى الْعَالَمِينَ فَحَسَدَهُ الشَّيْطَانُ فَكَانَ مِنَ الْغَاوِينَ ثُمَّ حَسَدَ قَابِيلُ هَابِيلَ فَقَتَلَهُ فَكَانَ مِنَ الْخَاسِرِينَ وَ نُوحٌ (عليه السلام) حَسَدَهُ قَوْمُهُ ثُمَّ حَسَدُوا نَبِيَّنَا (صلى الله عليه و آله) أَلَا وَ نَحْنُ أَهْلُ الْبَيْتِ الَّذِينَ أَذْهَبَ اللَّهُ عَنَّا الرِّجْسَ وَ نَحْنُ الْمَحْسُودُونَ كَمَا حُسِدَ آبَاؤُنَا."

Daga Amirul-muminina Ali (A. S) cikin kafa hujjarsa ga masu warware alqawari (daga cikin Sahabbai) cikin Khudubar da yayi yayin da suka warware ta, yace :

" HAQIQA ALLAH YA UMARCE KU DA KU MAYAR DA AL'AMARI ZUWA GA ALLAH DA KUMA ZUWA GA MANZONSA (S. A. W. W) DA KUMA ZUWA GA MA'ABOTA AL'AMARI DAGA CIKINKU. MASU FAYYACE ILIMI, KUMA KUKA TABBATAR (cewa za ku aiwatar da wannan umarni ), SA'AN NAN KU KAYI JAYAYYA. KUMA ALHALI ALLAH YA CE MUKU :

" KUMA KU CIKA MIN ALQAWARINA ZAN CIKA MUKU ALQARINKU (wanda Nayi muku),  KUMA GARE NI KUJI TSORO."

LALLE AHLUL-KITAAB DA  HIKIMA DA KUMA IMANI DA IYALAN IBRAHIM (A. S) ALLAH YA BAYYANAR DASU GARE SU SAI SU KAYI HASSADA, SAI ALLAH WANDA AMBATONSA YA 'DAUKAKA YA SAUKAR DA :

" SHIN, KUNA YIWA MUTANE HASSADA NE BISA ABINDA ALLAH YA BA SU NA DAGA FALALARSA  ? HAQIQA MUN BAIWA IYALAN IBRAHIM LITTAFI DA HIKIMA, KUMA MUKA BA SU MULKI MAI GIRMA. DAGA CIKINSU AKWAI WANDA YAYI IMANI DASHI, KUMA DAGA CIKINSU AKWAI WANDA YAYI SADDU (kau da kai) DAGA GARE SHI, KUMA JAHANNAMA TA ISA ZAMA SA'IRA (wutar da za qona masu warware alqawari. "

TO, MUNE IYALAN IBRAHIM (A. S), HAQIQA KUNYI MANA HASSADA KAMAR YADDA KUKA YIWA UBANNINMU. FARKON WANDA YA YIWA ADAMU (A. S) HASSADA WANDA ALLAH MAI GIRMA DA DAUKAKA YA HALICCE SHI DA HANNUNSA KUMA YA BUSHI GARE SHI DAGA RUHINSA, KUMA MALA'IKU SU KAYI MASA SUJADAH KUMA YA SANAR DASHI SUNAYEN ABUBUWA, KUMA YA FIFITA SHI AKAN TALIKAI, SAI SHAIDAN YAYI MASA HASSADA, SAI YA KASANCE DAGA CIKIN HALAKAKKU. 

SA'AN NAN QABILA YAYI HASSADA GA HABILA YA KASHE SHI, SAI YA KASANCE CIKIN MASU HASARA. 

DA KUMA NUHU (A. S) MUTANENSA SUNYI MASA HASSADA, SA'AN NAN SUKA YIWA ANNABINMU (S. A. W. W) HASSADA. 

TO, KU SAURARA  ! LALLE MUNE AHLUL-BAIT WADANDA ALLAH YA TAFIYAR MANA DA QAZANTA, KUMA MUNE WADANDA AKE YIWA HASSADA KAMAR YADDA AKA YIWA IYAYENMU HASSADA. "

المصدر :  بحارالأنوار، ج32، ص96/ الاحتجاج، ج1، ص160 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج3، ص222

Lalle duk wanda yayi hassada ga wannan falala wacce Allah ya yiwa iyalan gidan Manzon Allah (S. A. W. W) kuma ya juya musu baya har ya mutu akan haka tabbas babu shi babu Aljannar Ubangiji. 

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da ✍🏽Ado Isah Guda. 

          (08137925034)

20th November, 2023/  7th Jimada-Ulah, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post