Dambarwa Tsakanin Kamfanin Ɗangote Da Bua.

 



Daga Mahadi Tukur Almizan.


A safiyar yau Asabar 4 ga watan 11 na wannan shekara da muke ciki ta 2023. Aka wayi gari da labaran sukar juna tsakanin manyan kamfanonin Najeriya biyu, wato kamfanin Ɗangote da kuma kamfanin Bua.


Da farko dai kamfanin Ɗangote ya zargi kamfanin Bua da ɗaukar nauyin yaɗa labaran ƙarya akan kamfanin na Ɗangote.


Kamfanin na Ɗangote yayi zargi ne a lokacin da yake musanta zargin cewar ya sanya kansa cikin haramtacciyar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje.


Kamfanin na Ɗangote ya gargaɗi masu yaɗa irin wannan labarai, inda ya bayyana cewa yaɗa irin waɗannan labarai yima ƙasa zagon ƙasa ne. Ya shawarce su da su kaucema yin hakan.


Abinda ya haddasa wannan magana dai shine labarin da aka wallafa a kafofin sadarwa da ke zargin cewa shugaban kwamitin musamman da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kafa wato Jim Obazee domin binciken badaƙalar babban bankin Najeriya (CBN)  da ta gudana a ƙarƙashin shugabancin tsohon Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, a labaran da aka yaɗa an nuna cewa kamfanin na Ɗangote na da hannu wajen wannan badaƙalar da ta'ammuli da kuɗaɗen haramun.


Sai dai kamfanin Ɗangote ya zargi kamfanin Bua da hannu a cikin yaɗa wannan labarai da kamfanin ya bayyana a matsayin labaran ɓata suna.


Kamfanin Ɗangote ya bayyana cewa tun a shekarar 2016, aka fara yaɗa irin waɗannan labarai na ƙanzon kurege domin ɓata masa suna a jaridar Leadership da BusinessDay.


Ɗangote ya bayyana cewa makamantan waɗannan  labaran da aka yaɗa a ranar 14 ga watan Maris ɗin shekarar 2016, da aka wallafa a jaridar BusinessDay da Leadership, gidajen jaridun sun tabbatar da cewa kamfanin Bua ne ya ɗauki nauyin buga labaran.


A wancan lokacin an wallafa labarin da ke cewa kamfanin na Ɗangote ya karkata Dala Biliyan 3 na kuɗaɗen ƙasashen waje zuwa wasu kamfanonin shi dake wajen Najeriya.


Sai dai ana shi ɓangaren kamfanin Bua ya musanta wannan zargi inda ya bayyana cewa tun tsawon shekaru 32 da suka gabata Ɗangote ke yi masu zagon ƙasa.


Bua ya bayyana cewa wannan takun saƙar ta samo asali ne tun watan Agustan shekarar 1991 lokacin da suka yi aniyar bunƙasa samar da sikari (Sugar), wanda a wancan lokacin yayi ƙaranci a ƙasar nan.


Bua ya bayyana cewa zagon ƙasan da Ɗangote yayi masu a wancan lokacin shine ya bayyan sun samu lasisin samar da sikari sai Ɗangote ya nuna zai sayi sikarin a hannun su, sai dai da ya tashi biyan kuɗi sai ya ba su cak ɗin bogi na bankin Society General, sai da suka je cire kuɗi sai aka gane cewa lallai babu kuɗi a asusun da Ɗangote ya basu, wanda hakan yasa aka maka kamfanin na Bua a kotu, hakan yasa aka rufe kadarorin kamfanin, aka rufe asusun ajiyar kuɗaɗen kamfanin har na tsawon watanni uku.


Wannan dai shine zagon

ƙasan da kamfanin na Bua ke zargin kamfanin Ɗangote da aikatama kashi tun shekarar 1991.


©️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post