Daga Cikin Wasiyar Imam Khomaini Ga Matasa.
- Shaikh Abba Bature
1- Ku Tsaida Sallah Biyar a Kowace Rana,Kuma Kuyita a Cikin Lokacinta,Kuma Abu Ne Mai Kyau Ku Hada Da Yin Sallar Dare.
2- Ku Lizimci Azumin Litinin Da Alhamis Daidai Yadda Zaku Iya.
3- Karku Yawaita Yin Bacci,Kuma Ku Yawaita Karatun Al Qur,ani Dayawa.
4- Idan Kukayi Alkawari Ku Cikashi.
5- Ku Bayar Da Sadaka Ga Mabukata.
6- Ku Guji Zuwa Gurin Da Idan Aka Ganku Zaku Zama Abin Tuhuma.
7- Karku Zama Masu Al Mubazzaranci Idan Zakuyi Hidima,Kuyi Daidai Gwargwadon Misali.
8- Idan Zaku Saka Kayan Sawa,Ku Saka Wayanda Basuda Tsada Kuma Bana Alfahari Ba.
9- Ku Yawaita Yin Riyada ( Training ) Musammam Tafiya a Kasa Da Hawan Dutse Da Shiga Gulbi....
10- Ku Koyi Mabambantan Ilmomi Na Addini Dana Zamani.
11- Ku Koyi Yaren Larabci Da Kaidojinsa Domin Sanin Addininku.
12- Ku Yawaita Karatun Littatafai Na Addini Dana Zamantakewa Da Siyasa Da Falsafa.
13- Kuzama Masu Mantawa Da Aikin Alkhairin Da Kukayi Kuma Masu Yawan Tunawa Da Ayyukan Zunubi Domin Tuba.
14- Kuzama Masu Binciken Halin Da Ake Ciki Na Yau Da Kullum, Musammam Abinda Yashafi Musulmi.
Allah Ya Tabbatar Damu Akan Tafarkin Shiriya.